Zamuyi alfahari da matasanmu wajen cigaban Nijeriya

0

Zamuyi alfahari da matasanmu wajen cigaban Nijeriya

Inji Mista Zulu

Da yake jawabi wajen taron zaburar da matasa da Gwamnatochi dangane da kula da rayuwar matasa, Mista Zulu Daraktane na Kungiyar Kwadago ta Duniya dake kula da wasu yankuna a nan Afirika kamar Nijeriya Ghana Liberia da Sierra-Leone.

Yace; kulawa da rayuwar Matasa ya zama wajibi a garemu saboda idan akayi la’akari da yanayin zamantakewan rashin aikinyi garesu Babban hatsarine a garemu da qasashenmu. samar da aikinyi garesu zaman Lafiyarmu ne ,dama nahiyarmu baki daya.

Mista Zulu yace idan akayi la’akari da yawan matasa dake Nijeriya suna bukatar ayyukan yi da zasu gudanar da rayuwarsu na yau da kullun .

Taron da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a Birnin Tarayyan Abuja ya hada da wasu kungiyoyi na Duniya kungiyar Kwadago ta Duniya da Ma’aikatan matasa da wasanni ta Nijeriya da kuma masu fada aji daga kungiyoyin dabam- dabam.

Taron ya maida hankali ne kan yadda matasa ki gudanar da rayuwar zaman kashe wanda ba tare da aikinyi na fari ko baki ba , a nan gida Nijeriya.

Dayake jawabi ga mahalarta taron Sakataren dindindin a Ma’aikatan Wasanni da Matasa ta Nijeriya Mista Adesola Olusade yace; yanzu haka muna fuskantar kalubale yadda qasarmu take da tarin matasa masu yawan gaske amma dayawansu basu da aikinyi.

Yace; da dama an sake qananan sana’o’in wadanda aka gada daga Iyaye da kakanni. Kowa yana bukatar ayyukan jin dadi wanda zaiyi kudi yanzu yanzu.

Tunda farko Sakataren na dindindin saida yayi godiya masamman ga wadanda suka shirya wanan taron da kuma wadanda suka samu halarta taron.

Shima Mista Sukti Dasgupta Babban Ma’aikaci a Ofishin kungiyar Kwadago ta Duniya yace; samar da Ilumin ayyukan yi kamar aikin kere keren zamani da ake amfani dasu yanzu. da harkan kasuwanci da Sana’a zaman kamar sabbin fasaha ire-iren kerekeren zamani kera abubuwan da jama’a ke amfani dasu rinin kaya abubuwane da ya kamata Gwamnotochi su mai da hankali wajen bunqasa shi a Jihohin su saboda matasa su samu aikinyi. Masamman koyar dasu tun daga Makarantun Kwalaji.

Ya kara da cewa Kungiyar Kwadago tana bukatar bada gudumawa wajen kirkirar ayyukan yi wanda zai taimakawa dubban matasanmu dake rayuwa babu aikinyi.

Tattaunawar da ya hada kungiyoyi da masu fada aji da vangaren Gwamnati da MDD ya tsaida matsaya yadda za’a samu a fidda rayuwar matasa daga kunci da zaman kashe wando.

Yace; kafin shekarar 2030 zamucimma wanan kudurin na rage yawan iftila’o’in da muke tattare dasu na matsalar matasanmu da kashi 15 .

Shima Ministan Kwadago ta qasa Sanata Chris Ngige yace; ma’aikatansa tana ta kokarin pfarfado da makamancin wanan kudurin da zai samar da ayyukan yi ga yan qasa.

Yace; yawan matasan da muke dasu basu amfanar qasar da komai shiyasanya tattalin arziki qasarmu yake komawa baya a ko da yaushe . saboda duk qasar da take da tarin matasa kuma basu da ayyukan yi to qasar bata tasum cigaba a tattalin arziki.
Amma samun aikinyinsu shine cigaban tattalin arziki qasa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here