ZIYARA KASAR NIJAR: ME YA SA GIDAN TALABIJIN NA NTA NA KASA YAYI WA MASARI HAKA?
Daga tasakar labarai
A jiya talata 18/12/2018 kasar Nijar tai bukin cika shekaru sittin da zama kasar, kasaitaccen bukin ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu mukarabban gwamnatin tarayya cikinsu har da gwamnoni da ga tarayya Najeriya guda hudu.
Cikin gwamnonin harda gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, an yi buki kasaitacce kuma an yi ma shugaban kasa gagarumar taraya ta mutumci.
wani abin ban haushi da takaici da ya faru wanda ke bukatar bincike da tamabaya shi ne yadda kafar tashar talabijin ta NTA kin nuna hoton gwamnan Katsina cikin bakin da suka halarta.
gidan talabijin na NTA sun yi labarai kashi-kashi suna nuna baki daga Nijeriya da suka je tare da shugaban kasa, sun nuna kusan duk tawagar amma da sun zo wajen da gwamnan Katsina ya ke sai su dauke kamarar.
Gidan na talabijin sun kuma yi hira da duk gwamnonin da suka raka shugaban kasa amma ban da gwamnan na Katsina kamar yadda suka nuna har da maimaitawa.
Hatta wajen yanka kek na cikar kasar wadannan shekarun an nuno duk gwamnonin ban da gwamnan Katsina ko me yasa NTA suka yi haka?
Duk wanda ya kalli labaran da NTA suka nuna zai dauka tafiyar ba a yi ta tare da gwamnan Katsina ba, amma dan Katsina da wanda yaje wajen ne kawai zai san cewa gwamnan yaje kasar Nijar daga Katsina da tawaga mai karfin gaske cikinsu har da sakataren gwamnati, da hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Bara’u Mangal.
Binciken Taskar labarai ya jiwo wasu dalilan hakan wanda jaridar bata tabbatar ba. Shi ya sa bata kawo su ba.
Mun aika wa Femi Adeshina kakakin shugaban kasa wanda yana a wajen har hira dashi NTA sun yi, akan me yasa hakan har zuwa rubuta rahoton basu bada amsa ba.
———————————————————————————-
Taskar labarai jarida ce mai cikakkiyar rijista da ke bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma shafukan sada zumunta na facebook da Twitter da Instagaram da Youtube da layin whatsapp 07043777779