An kama wasu gungun ƴan fashi da makami a jihar Kebbi

0

An kama wasu gungun ƴan fashi da makami a jihar Kebbi

Rundunar ƴan sandar jihar Kebbi ta gudanar da taron mamema labarai a babbar hedikwata ranar juma’a ta inda kwamishin Kabiru Ibrahim ya gargaɗi ƴan dabar siyasa cewa duk wanda aka kama da makami a wajen yaƙin neman zaɓe zai gamu da fushin hukuma domin rundunarsa za ta gurfanar da shi a gaban Kotu, kuma ya ja kunnan duk wasu mara gaskiya a ko’ina suke a cikin jihar Kebbi su tuba su daina aikata laifi ko su kwashe tarkacensu su bar jihar Kebbi domin rundunar sa ba za ta lamunci aiyukansu ba.

Kuma ya ce jami’an ƴan sanda na jihar Kebbi
ta karɓi koke koke kan aikata manyan laifuka kamar fyade, fashi da makami, da kisan kai har guda 109. Ya ƙara da cewar rundunar ta kama mutune 872 bisa tuhumar aikata laifi inda ta gurfanar da mutane 872 a Kotu, an sami mutune 422 da laifi kuma suna kurkuku, lokacin da mutane 450 ke jiran shari’a, ƴan sndan sunyi nasarar kama babura 26, bindigogi 9, bindigu ƙirar harba sheka 10, ƙananan bindigu hannu 4 da sauran tarin makamai.

Kwamishina Kabiru ya zagaya da ƴan Jarida domin nuna musu kayan da suka kama, ciki har da waɗanda suka ƙwace mota a hannun wani Likita daga jihar Kaduna kwanaki 6 da suka gabat, kuma aka kamasu a jihar Kebbi sai kuma wani da ke cikin ƴan fashi da suka shiga gidan wani Alhaji a ƙauyen Sandare cikin satin da ya gabata har aka kashe ƴan fashi biyu
daga cikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here