MARTANI KAN BAYANIN DA DANDALIN APC BIYAYYA FORUM, TA FITAR A KATSINA RANAR 22 GA DISAMBA, 2018.

0

MATASAN KATSINA MASU SON CANJI
(KATSINA YOUTHS FOR SUSTAINABLE CHANGE) (KYSC).
MARTANI KAN BAYANIN DA DANDALIN APC BIYAYYA FORUM, TA FITAR A KATSINA RANAR 22 GA DISAMBA, 2018.
“ … Darakta-Janar na SMEDAN da Manajin Darktan FMB ne kawai suka ba da tallafin karfafa gwiwa don samun nasarar tafiyar sake zaben SHUGABA MUHAMMADU BUHARI a 2019…”

A iya saninmu wannan ikirari da ke sama, wanda aka jingina shi ga Mai girma Gwamnan jihar Katsina da Ciyaman na jam’iyyar APC a jihar Katsina karya ne, kuma kwata-kwata ba gaskiya ba ne!

Manajin-Daraktan Hukumar tashoshin jiragen ruwa (NPA), HAJIYA. HADIZA BALA USMAN ta hanyar ayyukan taimakon jama’a da Hukumar NPA take yi, tare da hadin gwiwar kungiyar da muka ambata a sama, KYSC, sun ba da tallafi mafi tasiri a jihar Katsina.

HAJ. HADIZA BALA USMAN ta ba da gudummawa da tallafi ga raunana da marasa galihu a al’ummarmu a dukkanin Kananan Hukumomin jihar Katsina. Wadannnan ayyukan sun kama daga samar da kujeri a makarantun firamare, samar da fitilu masu amfani da hasken rana da barguna 280 ga makarantun almajirai, samar da kekunan dinki, injin markade ga mata da famfunan injinan ban ruwa ga manoman karkara kamar yadda yake bayyane a kasa.

Hajiya Hadiza ta ba da gudummawa fiye da kowane dan siyasar da aka ba shi mukami a tarihin jihar Katsina, a matakin jiha ne ko na Tarayya wajen ba da tallafi da gudummawa ga raunana a al’ummarmu.

GA JERIN WASU AYYUKAN DA HAJIYA HADIZA BALA USMAN TA YI A JIHAR KATSINA KAMAR HAKA:

1. An ba da kujeri 4,000 ga makarantar firamare ta Musawa.

2. An gina azuzuwan karatu a Musawa da Jikamshi.

3. An rarrabar da injin makarde guda 40 a Karamar Hukumar Musawa.

4. An ba da N25,000.00 kowanne ga matasa 50 a Karamar Hukuma.

5. An rarraba injinan famfunan ban ruwa guda 40 a Karamar Hukumar Musawa.

6. An rarraba kekunan dinki guda 50 ga mata a Karamar Hukumar Kafur.

7. An rarraba injinan ban ruwa guda 50 a Karamar Hukumar Dandume.

8. An rarraba injinan ban ruwa guda 50 da injinan markade guda 50 a Karamar Hukumar Katsina.

9. An rarraba injinan markade da na dinki guda 70 a Karamar Hukumar Katsina.

10. An rarraba injinan ban ruwa guda 50 na Karamar Hukumar Sandamu.

11. An rarraba kekunan dinki da injin markade 10 a Karamar Hukumar Daura.

12. An rarraba kekunan dinki guda 50 a Karamar Hukumar Malumfashi.

13. An rarraba kekunan dinki guda 50 da injinan markade guda 50 a Karamar Hukumar Ingawa.

14. An bai wa mata 200, mata 20 a shiyyar Funtua (Kananan Hukumomi 11) kaji masu yin kwai, wanda aka yi a Funtua.

15. An rarraba barguna 4,000 ga makarantun Almajirai a duk fadin Kananan Hukumomin jihar Katsina, inda aka kaddamar a Karamar Hukumar Daura.

16. An kakkafa fitilu masu amfani da hasken rana guda 282 ga makarantun Almajirai 282 a duk fadin Kananan Hukumomin jihar Katsina guda 34.

17. An ba da motar Bas ga kungiyar FUTURE ASSURED Organization wacce Haj. Ambaru Wali take shugabanta.

Dukkan wadannan ayyukan taimakon jama’a a sarari suke kuma za a iya tabbatar da su, da ma an ce GASKIYA BA TA NEMAN ADO.

A karshe, HAJIYA HADIZA BALA USMAN, wacce ta fito daga gidan da aka san su da neman tabbatar da adalci da daidaito a al’umma, za ta ci gaba da jajircewa wajen taimakon matalauta a al’ummarmu duk da irin wannan farfaganda na karya, wanda ba zai rage ta da komai ba saboda wadanda suka ci gajiyar ayyukanta za su ci gaba da yaba mata da godiya gare ta a yunkurinta na tabbatar da sahihin canji mai dorewa a jihar Katsina da kasa Nijeriya gabaki daya.

Daga ALH. SALLAU ARAWA
D.G. 1 KYSC KATSINA
08032515386

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here