LABARI DA HOTO MAI BAN TAUSAYI: YADDA AKA KASHE WANA AKA KONA GAWARSA A GABA NA!
…………………………..Inji Sagir Isah
Daga Taskar Labarai.
Sagir Isah Mobil ya yi tattaki har ofishin Taskar labarai dake Katsina, cikin murya mai ban tausayi da nuna hotuna masu daga hankali, da wa’azi ga mai lura, ya bada labarin daki-daki yadda dan uwansa Ali Isah Mobil da Alhaji Usman Aliyu aka kashe su a gabansa kuma aka sanyawa motar wuta, Alhaji Usman Aliyu ya kone da ransa yana kallo, sannan wani maras imani ya daga bindiga ya kara harbin wansa Ali Isaha Mobil
ta’addacin da ake zargin fulanin Daji masu satar mutane ne suka aiwatar.
Sagir ya fada cikin murya ta ban tausayi cikin sheshshekar kuka idan ya tuno al’amarin, a ranar 29/11/2018.
Ina zaune a garin Gurbi ta jahar Zamfara sai dan uwana, yayana yayi mani waya, mai suna Ali Isa Mobil wanda yake direba ne a gidan Alhaji Lawal Dahiru Mangal, yace mani gashi nan zai wuto Katsina daga Sokoto don haka in ina zuwa in shirya zasu dauke ni a Gurbi mu wuce , nace to
suka iske ni gaf da magrib suna gaba ina baya a cikin mota Toyota Corrolla LX, muna tafiya mun wuce wata hanya data hada Nijar da Nijeriya wadda masu shigo da kaya da kuma motoci kan biyo, sai muka ga jerin wasu fulani masu yawan gaske a bisa mashina suna ketara hanya wadansu da bindigogi a rataye a kafadunsu.
suka daga mana hannu, amma sam bamu lura ba, Mun zo dai-dai wata kwana sai kawai muka ga wasu fulanin a gabanmu wasu a gefen hanya wasu a tsakiyar hanya .
Ba wata magana, sai kawai mukaji an bude mana wuta , nan take sai motar tamu ta nufi daji aka billar dani aka jefar dani gindin wata geza, su kuma yan uwana guda biyu daya aka billar da shi gefen motar, wani ya harbi tankin motar ta kama da wuta.
Daga inda nake, sake sai na ga, duk Fulani sun nufo inda motar take, suka iske Ali Isah Mobil a waje motar ta billar da shi, nan wani ya kara daga bindiga ya dirka masa.
Alhaji Usman Aliyu yana cikin mota da ransa, suka kara harbin tankin motar ta kara kamawa da wuta, Alhaji usman Aliyu yana ciki ya kama da wuta ya canye.
ina jin suna cewa, su kadai ne ko akwai wasu? aka ce su kadai ne, sai naji ana cewa kuyi maza mu wuce kun san inda zamu yi aikin nan fa ba nan bane.
Daga nan sai naga sun wuce, can da naji kafa ta dauke , na zo wajen motar na gansu duk sun mutu, na samu yadda na samu wasu sojoji muka zo dasu aka dau hotuna, yadda abin ya faru. Suka ce muje akai rahoto wajen ‘yan sanda daga nan na kira gida Katsina. aka je aka dauko gawarwakin aka zo dasu Katsina in da akayi masu jana’iza aka rufe su a makabartar Danmarna.
A wannan labari a kwai hotunan gawarwakin masu ban tausayi.
gawar Alhaji Usman Aliyu ta kone kurmus, kamar yadda zaku ga sai dai tokarta da kashi aka dauko, ita kuma gawar Alhaji Isah duk ga alamar harbi a jikinta.