WACECE LADI KWALI TA JIKIN NAIRA ASHIRIN 20?
_Muhammad Bala Garba, Maiduguri._
‘Yan Najeriya da dama basu san labarin matar da aka sanya hoton ta a bayan naira 20 da suke kashewa a yau da kullum ba.
Matar da hoton ta ke bayan naira 20 na kudin Najeriya wata fitacciyar mai sana’ar kera tukwane ce mai suna Ladi Kwali.
An haife ta a shekarar 1925 a kwauyen Kwali, wanda yanzu haka yana Area Council na baban birnin taraya Abuja dake Nijeria. (Wasu masana tarihi kuma sunce shekarar haihuwar ta 1920 ne).
Ladi Kwali ta taso ne a gidansu inda mata ke sana’ar kirar tukwane don su sami abin da zasu tallafawa kansu. Itama ta koya sana’ar wajen kanwar mahaifiyarta tun tana karamar yarinya.
Tun lokacin da take karama tana da matukar hazaka wajen kirar tukwane da wasu abubuwan, galibi ma mutane kan saye tukwanenta tun kafin ta kai kasuwa.
Da taimakon wani dan kasar Ingila mai sha’awar daukan hotunan tukwane mai suna Michael Cardew, Ladi Kwali tayi suna a duniya a shekarun 1950 miladiyya. A shekarar 1951 aka nada Michael Cardew a matsayin jami’i mai kula da kera tukwane a ma’aikatan kasuwanci da masana’antu, inda ya kafa makarantar koyar da kera tukwane a Abuja tare da Ladi Kwali a shekarar 1952 miladiyya, sun kwashe shekaru 15 suna koyar da kera tukwane.
Tukwanen da Ladi Kwali take karewa sunyi suna saboda kyawun su da ingancinsu, hakan yasa Sarkin Abuja na wannan lokacin, Suleiman Barau ya saya tukwane da yawa daga wurinta don kayata fadar sa.
Ladi Kwali da Michael Cardew sun tafi ziyara a kasar Amurka da Landan inda ya gabatar da ayyukan ta a wurare da dama kuma mutane na ta sha’awa da mamakin irin baiwar da take dashi.
Ga kaxan daga cikin lambobin yabo da karamawar da ta samu:
1- A shekarar 1962 an karrama ta da MBE (Member of the Order of the British Empire), a kuma 1977 jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta karrama ta da digirin girmamawa na Dakta, (Honorary Doctorate).
2- Gwamnatin Najeriya ta karramata da lambar yabo mafi girma a Najeriya na ilimi wato ‘Nigerian National Order of Merit Award’
3- A shekarar 1981, ta samu lambar yabo na (OON) wato Officer of the Order if the Niger.
4- A sanya sunanta a wani layi a babban birnin tarayya Abuja wato Ladi Kwali Street.
5- An canja sunan makarantar koyar da kera tukwanen na Abuja zuwa Ladi Kwali Pottery.
6- An sanya hoton ta a bayan naira 20 na kudin Najeriya, ita ce mace ta farko da aka sanya hoton ta a kudin Najeriya.
Bayan Michael Cardew ya rasu a shekarar 1983, Ladi Kwali ta rasu a ranar 12 ga watan Augusta tana da shekaru 59 a duniya a garin Minna ta jihar Neja.
Ina kira ga xaukacin mata da su yunkura wajen koyi da Ladi Kwali.