YAR SHAKARU 24? MUSULMA YAR NAJERIYA?

0

WACECE YA MAIRA? MATUKIYAR JIRGI YAR SHAKARU 24? MUSULMA YAR NAJERIYA?


fassarar Abdurrahaman Aliyu
Daya Taskar labarai.

Kamar kowace irin mace, sunana Maira Umar Bishir, ni Kanuri ce daga jihar Barnonina da shekaru 24, ina sha’awar karance-karance da tafiye-tafiya da kuma kasancewa tare da iyalaina domin ina girmamasu.

Me ya sa kikayi sha’awar zama Mai tukin jirgi, kuma ya kike ji a yanzu?

Tun ina karama na ke sha’awa zama mai tuka jirgin sama, domin duk sadda naga ma’aikatan jirgin sama na kan samu farin ciki a raina. Kulum gurina in zama direbar jirhin sama.

Ya akayi kika shawo kan iyayenki suka aminta da wannan mafarki naki.

Gaskiya ban taba tunanin shawo kansu ba domin duk wasu bukatuna suna baningoyan baya, suma taimaka man sosai domin ganin mafarki na ya tabbata.
A takaice ina da mafarkin zama likita wannan yada duk lokacin da mahaifina zai dawo daga unguwa sai ta sawo man kayan wasa na likitoci.

A lokacin da na yanke shawarar zama mai tuka jirgin sama ban sha wahalar shawo kansu ba ?.

Ya mutane suka ji lokacin da suka ganki akaran farko matsayin mai tuka jirgin sama?

Mutane sun yi mamaki matuka kasancewa ta mace kuma daga arewacin Nijeriya, musamman yadda mahaifa na suka yarda na yi wannan karatu.

Ya kike tunanin ganin kanki nan da shekara biyar zuwa goma?

Da yarda Allah zan zama cikakkiyar direbar jirgi kuma Kaftin.

Shin Kinga wani na nuna bambanci da ake gwada maki a hukumar sufuri ta Kasa?

Tun da na fara tuki har zuwa yanzu ana samun karin mayukan jirgi mata daga arewacin Nijeriya. Musamman in muka yi la’akari da girman kasar Nijeriya da kuma darajjar da take da shi a Duniya, ina tunanin muna bukatar katuwar matuka jirgi mata musamman domin rage marasa aikin yi a kasar.
_____________________________________________________
Don labarai da bincike na musamman jeka shafin yanar gizo na Taskar labarai dake www.taskarlabarai .com da kuma zaurukan sada zumunta na.facebook.twiteer, instigram da you tube.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here