WANENE MARIGAYI ALHAJI SHEHU USMAN ALIYU SHAGARI?

0

WANENE MARIGAYI ALHAJI SHEHU USMAN ALIYU SHAGARI?

_Muhammad Bala Garba, Maiduguri._

An haifi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a kauyen Shagari dake Sokoto a shekarar 1925, shi ne d’a na shida a gun mahaifinsa Aliyu, magajin kauyen Shagari, wanda manomi ne, dan kasuwa yana kuma kiwo.
Allah ya yiwa mahifinsa rasuwa yana dan shekara biyar da haihuwa.
Alhaji Shehu Shagari ya fara karatun kur’ani tun yana dan shekara hudu, kuma daga bisani ya je makarantar Elimentari dake garin Yabo kusa da kauyen Shagari, daga nan kuma ya tafi makarantar Middle a Sokoto, daga nan kuma ya je kwaleji ta Kaduna.
Bayan da ya kammala karatun sakandirensa, Alhaji Shehu Shagari ya yi koyarwa a makarantun middle daban-daban a matsayin malamin kimiyya da ma tarihi.
Tun yana kwaleji Shagari ya fara nuna sha’awar shiga siyasa, inda a shekarar 1946 shi da Malam Gambo Abuja suka kafa wata kungiyar matasa a Sokoto, kuma sun samu goyan bayan dattijai kamar Sir Ahmadu Bello da Ibrahim Gusau da kuma Malam Ahamdu Dabbaba.
A shekarar 1948 ne kuma aka amince da a hade dukkanin kungiyoyin siyasar yankin zuwa kungiyar NPC wadda daga bisani ta zama jam’iyyar da ta tsaya takara a zaben shekarar 1959.
Kafin wannan shekarar ne aka zabi Shagari a matsayin wakilin mazabar Kudu-maso Kudancin Sokoto, kuma a shekarar 1958, an zabe shi a matsayin sakataren majalisar Fira minista, Sir Abubakar Tafawa Balewa.
Daga bisani Shagari ya rike mukaman minista daban-daban da suka hadan da na ci gaban tattalin arzuki a shekarar (1960), na kula da harkokin cikin gida a (1962) da kuma na ayyuka da safiyo a (1965).
Bayan juyin mulkin farko da sojoji suka yi, Alhaji Shehu Shagari ya koma gida Sokoto.
Da hawan janar Gowon sai ya baiwa Shagari ministan kula da harkokin tattalin arziki daga bisani kuma aka bashi ministan kudi.

*Mulkin Jamhuriya ta biyu a Najeriya*
A shekarar 1979 zuwa 1983 sojoji suka kwashe suna mulkin Najeriya kafin a kai ga kafa jamhuriya ta biyu bayan zaben da aka gudanar a cikin watan Yuli zuwa Agustan shekarar 1979, kuma ranar 1 ga watan Oktoban wannan shekarar janar Olusegun Obasanjo ya mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.
Jam’iyyu biyar ne suka tsaya takara a zaben da aka yi kuma yawancinsu birbishin na jamhuriya ta biyu ne.
Alal misali jam’iyyar NPN wadda ta lashe zaben tsatson jam’iyyar NPC ce wato Jam’iyyar Mutanan Arewa kodayake jam’iyyar NPN ta samu goyan baya daga jihohin kudu maso gabashin Najeriya wadanda ba na kabilar Ibo ba ne.
Jam’iyyar UPN ta samo asali ne daga jam’iyyar Action Group (AG) ta Yarabawa, wadda Cif Obafemi Awolowo ya ci gaba da shugabanta.
Jam’iyyar NCNC ta jamhuriya ta daya ce ta haifar da jam’iyyar NPP ta yawancin kabilar Ibo wadda Nnamdi Azikiwe ya shugabanta.
Sai jam’iyyar PRP ta marigayi Malam Aminu Kano wadda ta samo asali daga jam’iyyar NEPU a jamhuriya ta daya.
Akwai kuma jam’iyyar GNPP wadda Waziri Ibrahim daga jahar Borno ya shugabanta.
A lokacin da aka kafa jamhuriya ta biyu Najeriya na cike da kyakykywan fata, biyo bayan tashin farashin man petur a kasuwanin duniya, tare da samun karin kudaden shiga.
Sai dai kuma a tsakiyar shekarar 1981, murna ta koma ciki bayanda yawan kudaden da ake samu ta hanyar man fetur ya ja baya.
A lokacin wannan gwamnati, dubban manoman da aka kwacewa filayensu domin gina madatsar ruwa ta noman rani a Bakalori a jahar Sokoto sun yi ta yin zanga-zanga, inda ‘yan sanda suka far musu suka kona kauyukansu tare da kashe ko raunata daruruwan masu zanga zangar.
Bayan wannan kuma rikicin addini ko Mai Tatsine da aka yi a Kano da Kaduna da Maiduguri a shekarun 1980 zuwa 1982 ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Har ila yau a shekarar 1981 malaman makaranta sun gudanar da zanga-zanga bisa rashin biyansu albashi.
Domin samun bakin zaren warware matsalolin da kasar ta shiga, gwamnatin wannan lokacin ta sallami miliyoyin wadanda ba ‘yan kasa ba yawancinsu ‘yan Nijar da Ghana da nufin samawa yan Najeriya guraben aiki.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar, bayan kowace shekaru hudu za’a gudanar da zabe, don haka ranar 20 ga watan Agustan shekarar 1983, aka gudanar da zabe wanda hukumar zabe ta FEDECO ta bayana cewa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ne ya sake lashewa.
Mutane da dama basu amince da sakamakon zaben ba, abinda da ya jawo ‘yan rajin demokradiyya gudanar da zanga-zanga.
Ganin yadda al’amura suke dagulewa yasa ran jajiberan sabuwar shekara wato 31 ga watan Disambar shekarar 1983, sojoji suka yi juyin mulki, inda suka nadan janar Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasa.
Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya rasu ranar Juma’a 28 ga watan Disamba a shekarar 2018. Tsohon shugaban ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja inda yake jinya.
Alhaji Shehu Shagari ya rasu yana da shekara 93 a duniya, bayan ya sha fama da jinya.
Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983.
Muna addu’ar Ubangiji Allah ya gafarta masa yasa Aljanna ce makoma.

Ina mika sakon ta’anziya ga ilahirin al’ummar AREWA. Muhammad Bala Garba, Dan Maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here