YADDA AKA KAI HARIN GURBI: INA CIKIN GARIN

0

YADDA AKA KAI HARIN GURBI: INA CIKIN GARIN
………………………INJI SAGIR ISAH MOBIL

Daga Taskar Labarai

“Sunana na Sagir Isah Mobil ni kane ne ga marigayi Ali Isah Mobil wanda barayin shanu suka harbe da kona gawarsu a watan nawumba ta bara a hanyar Jibia zuwa Zamfara.

Ni dan Katsina ne amma ina zuwa harkar kasuwanci a garin Gurbi ta jahar Zamfara garin da kwanakin baya mahara suka kone duk wani abu mai amfani a garin, ina a cikin garin abin da ya faru ya faru nima da kyar na sha da rayuwa ta.

Ranar da abin zai faru muna a cikin garin Gurbi sai muka rika ganin wasu bakin fuska suna shigowa garin, amma ba wanda ya dauka sun zo da wata manufa suka tsaya duk wani waje mai muhimmanci a Garin.

Daga nan wasu, sai suka yi tun da a duk bakin shiga da fita garin, ashe duk suna sake da makamai,çan sai mukaji wani ya yi harbi sama alama, daga nan sai suka fara harbi sama,
Harin sai ya rude.

Wasu maharan na harbin mutane wasu kuma na harbin sama don firgita mutane wasu na kona motoci da muhimman gine gine.

Ni ma wani maras imani ya bini da harbi da niyyar kashe ni Allah ya tsare. Daga can sai aka ji suna wata alama ta fita gari, sai suka yi gungun suna fita, suna fadawa daji.

See also  ARMY DISMISSES TWO SOLDIERS OVER KILLING OF ISLAMIC CLERIC IN YOBE ... soldiers to face civil prosecution

Daga baya an fada mana cewa, waya akawo masu cewa ga sojoji nan tafe zuwa garin, Don haka sai suka rika nuna alama ga ‘yan uwansu mahara cewa su bar garin.

Wani da ya boye bisa itace, yaji maharan na bayanin cewa gayyato su akayi, su zo don rama wani kame da kisa da aka taba yi ma fulani a garin ranar kasuwa.

Wani yaji maharan na gardama da wadanda. Suka gayyato su, suna cewa, mun yi daku ba kisa ba kone kone sai dai firgitarwa kuma kuka amince a kan haka me ya sanya kuka saba?

Idan mai karatu, ya kalli hotunan da na hado da labarin nan zai ga irin barnar da suka aikata, zai gane yadda suka aikata tu’annati kafin su bar garin.

Bayan tafiyar su duk Inda ka duba kwafson alburushi ne a garin maharan wasu basa harbin mutane, sai ma su gwada masu yadda za su buya. Wasu ko harbi kawai sai dai Allah ya tsare ka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here