KIRA GA MATASA AKAN BANGAR SIYASA (I)

0

KIRA GA MATASA AKAN BANGAR SIYASA (I)

_Muhammad Bala Garba, Maiduguri._
A duniyar dimokradiya babu abun da ake amfani da shi wajan yaudarar al’umma a wannan zamani face sai an dangantasa da rayuwar matasa, kasancewar babu wani buri da matashi ke buqata face yaga ya tsinci rayuwarsa cikin sauki da samun ingancin rayuwa ta hanyar dogaro dakai.
Wajan neman saukin rayuwa ke durmiyar da wasu matasa ta hanyar kwadayi da gaugawar samun jin dadin rayuwa ne savavin tabarbarewar rayuwar matasa da samun damar wasu yan siyasa zuwa ga gurbatar da rayuwar matasa cikin sauki don amfani dasu wajan cin zarafi tallar karya da basu tarbiyar rashin kishin qansu da dagula rayuwar su.
Ina kira ga matasa damu hankalto, mutuna iyayenmu da ya’yanmu da malumanmu, gidajenmu ne a zagaye damu, hasali babu mai son mahaifansa da ya’yansa su shiga kuncin rayuwa da halin wai ni’ya’su, in hakane to yaci mu matasa mu shiga taitayinmu wajan yakar miyagun dabi’un da muka aro daga dimokradiya mu kawo zaman lafiya da cigaban al’umma ta hanyar zaven shuwagabanni nagari waxanda ke da burin ganin matasa sun zama Manyan Gobe.
Lokaci yazo da aka fara shiga yanayin siyasa a Najeriya, wato yayin da ake shirin gudanar da zavuka.
Siyasa na da mahimmanci a kowacce qasa ta duniya dake bin tafarkin democradiyya.
Dalili kuwa shi ne siyasar tsarin democradiyya na baiwa jama’a damar zabar wanda suke ganin ya dace da su, kuma wanda zai biya musu bukatun su da kuma share musu hawaye.
Jama’a kan ba da goyon baya ga wanda suka yi imanin zai wakilce su kuma wakilci na gari ba wanda zai je don wakiltar kan sa ba. Ta yaya jama’a ya kamata su tabbatar da cewa sun zavi na gari ba zaven tumun dare ba?
Insha Allahu nan gaba zan yi rubutu akan wannan batu. Amma yanzu ina so ne na yi kira ga matasa akan bangar siyasa.
Tun bayan da Najeriya ta koma tsarin democradiyya yau kusan shekaru goma sha takwas (18) kenan ‘yan siyasar qasar ke amfani da matasa domin cimma manufofin su na siyasa.
Ba laifi ba ne
‘yan siyasa su nemi goyon bayan matasa. Misali a shekarar 2008 miladiyya, quri’a da goyon bayan matasan Amurka ta taimaka wajen nasarar shugaban Amruka Barack Obama.
Abin da yake laifi shi ne amfani da matasa a matsayin ‘yan vangar siyasa domin samun nasara a zave. A zabukan da suka wakana a baya ‘yan siyasa a Najeriya na baiwa matasa kuxi, inda su kuma sukan sayi kwaya da sauran ababen sa maye da makamai, suna bi suna razanar da abokan hamayya da sauran jama’a.
A kan yi fito-na-fito tsakanin ‘yan bangar ‘yan siyasar. Wani lokaci ma a ji munanan raunuka, a wasu lokuta a rasa rayuka. Wannan abun takaici ne.
Shin matasan nan da suke bari ana amfani da su don cimma manufar zabe, duk da cewa sun san ‘yan siyasa zasu yi watsi da su, da zarar sun yi nasara. Sun san ciwon kan su kuwa? Suna da masaniya kan cewa ‘yan siyasa basu damu da su ba illa kawai sun mai da su tamkar matattakala ce da suke takawa domin “cin zave” ko ta halin kaka?
Amsar da nake so sani ita ce: ta ya ya ne matasa zasu jajirce su qi yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa qudi qalilan waxanda akewa kallon marasa mutunci a Najeriya, lamarin da kan iya sanadiyyar hasarar rayukan su da ci bayan qasar mu.
_Allah yasa mu dace._
Daga littafina mai suna *MANYAN GOBE.*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here