WACECE MARIGAYIYA AISHA LEMU?

0

WACECE MARIGAYIYA AISHA LEMU?

A takaice.

_Muhammad Bala Garba, Maiduguri._

An haifi marigayiya malama Aisha Lemu a garin Poole na yankin Dorset na kasar Ingila a 1940.
Tana da shekara goma sha uku (13) da haihuwa sai ta fara tunanin sauya addininta, inda ta fara da duba addinan Hindu da na Bhudda amma basu gamsar da ita ba.
Ta yi karatun jami’a a makarantar koyon al’adu da harsunan kasar Sin da na Afirka a jam’iar Landan (SOAS), inda ta karanta tarihi da al’adu da kuma harshen kasar Sin.
A jami’ar ne kuma ta fara haduwa da dalibai Musulmai wadanda suka rika ba ta litattafan addinin Musulunci, kuma ba da dadewa ba sai ta musulunta a shekarar 1961, a lokacin tana shekararta ta farko a jami’a.
A lokacin ne ta bayar da gudunmawarta wajen kafa kungiyar dalibai Musulmai na makarantar ta SOAS a jami’ar Landan, kuma ita ce sakatariyar kungiyar ta farko.
Bayan ta kammala karatun digiri na farko a jami’ar Landan, Aisha Lemu ta koma domin karatun babban digiri a kan harshen Ingilishi, kuma a lokacin ne ta fara ganin Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi kuma ya isa Landan ne domin karo ilimi a jam’iar ta Landan.
Malama Aisha ta rasu a ranar Asabar 5/1/2019, tana da shekara 79 da haihuwa bayan ta yi wata gajeruwar jinya.
Malama Aisha ta bada gaggarumar gudun mawa a addini musulunci musammanma ta wajen rubuce-rubuce.
Wannan babban rashi ne da musulmai muka yi na kundin ilimi mai muhimmanci wanda ba ya misaltuwa, idan mukayi duba da cewa karbar Musuluncin tayi, kuma Baturiya ce, amma ta tashi tsaye domin haskaka duhun jahilci ta hanyar amfani da hasken Musulunci.
Muna rokon Ubangiji Allah ya gafarta mata yasa aljannan ce makomarta ya albarkaci zuriyarta. Amin. _Dan Maiduguri._

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here