AYAR ALLAH A KOFAR DURBI KATSINA

0

AYAR ALLAH A KOFAR DURBI KATSINA

Daga Taskar labarai


A jiya laraba 9/1/2019 wani abin Al ajabi ya faru a gadar kofar Durbi da ke titin Nagogo hanyar zuwa tsohuwar gidan gwamnatin Katsina
Wajen karfe takwas na yamma..masu wucewa ta Bisa gadar a kafa suka lura da Ruwan da kan fito daga magudanar ruwa ta kofar marusa ..idan ya zo biyo ta gadar ta kofar Durbi, ya gangara ta magudanar da zata nufi kofar sauri..sai Ruwan yayi kumfa …kumfar sai ya rubuta Allahu da larabci ..wani kumfan kuma sai ya Rubuta Muhammadu da larabci.
Mutanen da suka fara lura sai suka Rika gangarawa Don suga tabbas cewa idonsu ba zagi yake ba..da suka Isa har wajen Ruwan suka ga cewa .Tabbas rubutun Haka ne..sai aka fara yekuwar ga jama a suzo suga abin Al ajabi.kafin kace meh ..daruruwan mutane sun cika wajen .
Wani abin mamaki idan kumfar ya rubuta Allahu da Muhammadu..sai jama a su wawashe su kwashe kumfar su shaye Ruwan..sai kuma wani kumfar ya sake yin Rubutun
Wani malami da aka Kira shi yazo yaga Ni da idonshi..Yana zuwa ya karanta ya tabbatar da abin ikon Allah ne ..sai kawai ko rigarsa bai cire ba yayi kurmiye cikin Ruwan yayi wanka sosai duk da sanyin da ake tsagawa a cikin Daren.
Daya daga cikin wadanda suka ga Al ajabin ..cikin dare lokacin an cika ana mamaki ..har da Dan wairen Katsina Alhaji sada Salisu Ruma ..kamar yadda ya tabbatar wa da Taskar labarai.
Dakta Muttaqa Rabe darma ..shima yazo wucewa yaga anyi cincirindo ya tsaya .ya gane ma idonsa abin Al ajabin
Ruwan ya bar zana sunayen na Allahu da Muhammadu..Bayan wasu awanni.yana zanawa ana kwashewa.
Da safiyar​ Alhamis 10/1/2019..jama a na ta zuwa .suna ganin Inda wannan abin mamaki.ya faru.amma tun Daren. Laraba sunayen suka bar fitowa.
Da yake lokacin waya ne, tun Daren akayi ta daukar hotuna a waya ..na rubutun..wasu hotunan cikakken rubutun wasu kuma ba cikakku ba, da ya ke da kumfar ya fito kwasa akeyi a shanye ..Yana fitowa wasu na jiran su kwasa.haka akai tayi har ya bar fitowa.
Taskar labarai taji ra ayin malamai akan Wannan ..Inda duk bakinsu ya hadu akan cewa .Allah Yana ganin damar bayyana ayarsa a Inda yaso.kuma a lokacin da yaso.
Illa kawai suka gargadi .Al umma kar a. Maida ayar Allah abin shirka da Allah .ita ayar Allah ta Zama abin Kara imani da Allah ne.da Yi Masa da a..
Ga wasu hotunan da Taskar labarai ta samu..na zanen da kumfar ya rikayi…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here