NAGARTACCEN WAKILI.
Daga Muhammad Bala Garba, (Alh Bawayo).
08025552507
Tun bayan da Najeriya ta koma tsarin democradiyya yau kimanin shekaru Ashirin (20) ba’a tava samun matashin dan siyasa mai farin jini kamar Injiniya Abdulsalam Mustapha Kachallah ba.
Injiniya Abdulsalam dan takarar majalisar tarayya ne mai wakiltar birnin Maiduguri a inuwar jam’iyyar PDP (People’s Democratic Party).
Birnin Maiduguri dai shi ne babban birnin jihar Barno a arewa maso gabas din Najeriya. Maiduguri ita ce birnin da tafi kowane birni girma da yawan jama’a a arewa maso gabas din Najeriya. A qalla birnin yana da jama’a fiye da miliyan daya. Birnin na Maiduguri an kafa shi ne a shekarar alif daya da dari tara da bakwai (1907). Maiduguri ta ‘kunshi unguwan Yerwa (Yerwa yana nufin alheri a harshen kanurai (Barebari)) ta yamma da kuma tsohuwar Maiduwuri ta bangaren gabas.
Daddazon jama’a ke nan daga unguwanin Bulabulin da Bolori I da Bolori II da Fezzan da Gwange I da Gwange II da Gwange III da Gamboru Liberary da Hausari/Zango da Limanti da Lamisula/Jabbamari da Maisandari da Mafoni da Shehuri Sourth da kuma Shehuri North suka fito kwansu da kwarkwatansu matansu da mazansu yaransu da manyansu suke nuna goyon baya xari bisa xari ga Injiniya Abdulsalam Mustapha Kachallah.
Siyasa na da mahimmanci a kowacce qasa ta duniya dake bin tafarkin democradiyya. Dalili kuwa shi ne siyasar tsarin democradiyya ne na baiwa jama’a damar zabar wanda suke ganin ya dace da su, kuma wanda zai biya musu bukatun su da kuma share musu hawaye irin su Injiniya Abdulsalam.
Jama’a kan ba da goyon bayansu ga wadanda suka yi imanin zasu wakilce su kuma wakilci na gari irin su Injiniya Abdulsalam, ba irin wadanda zasu je don wakiltar kan su ba.
Injiniya Abdulsalam mutum ne mai son jama’a da taimakonsu, yana dauke da dawainiyar karatun matasa bila-adadin a ‘yan birnin Maiduguri, domin kuwa duk wata qasa da ta ci gaba a wannan duniya, idan ka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan ci gaba, za mu ga a hannun matasansu ya ke. Saboda basu yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasa ba, wannan yasa Injiniya ya zare dantse wajen kulawa da karatun ya’yan al’umma. A dalilin wannan ne yasa ake masa laqabi da ABDULSALAMU NA YAN MAKARANTA.
Al’ummar birnin Maiduguri suna cewa “Ratan dake tsakanin Injiniya Abdulsalam da abokin hamaiyarsa ta jam’iyya mai mulki tamkar ranta dake tsakanin shugaba Muhammadu Buhari ne da Atiku Abubakar”.
Al’ummar qasar Najeriya na shirye-shiryen gudanar da zaben shekarar 2019, sai dai bana zaben yazo da wani irin sallo domin al’umma sun ce babu wani sak da zasuyi, mutum zasu zava ba jam’iyya ba, zasu zavi wadanda suka cancata ne irin su Injiniya Abdulsalam, koda kuwa basa kaunarsu, zasu zabi wadanda Najeriya ce a gabansu ba wasu sashe na mutane ko kabila ko wata kungiya ba.
Ina kira ga al’ummar Najeriya mu farka! Mu kuma yi kyakyawan nazari da tunani akan me zai faru damu tsawon shekaru hudu idan muka dangwala wa wane kuri’armu? Shin biyan bukatar da zamu samu da yan dubunnan da zai bamu mu siyar da yancinmu zai wadace mu har tsawon shekaru hudu! Shi zai taimaka mana idan aka kamu asibiti ko muka kai kanmu? Zai ciyar da mu da iyalanmu har tsawon shekaru hudu? Zai samarwa da ‘ya’yanmu ilimi wadatacce? Zai inganta rayuwarmu da rayuwar wadanda suke karkashinmu? Zai samar mana da cikakken tsaro da aminci a gidajenmu? Mu tuna makomar al’umma duka a hannunmu yake, shin cigaba zai zame mana ko ci baya? Ya zama dole muhimanta wannan damar da muke da ita mu zabi wadanda suke son ci gabanmu kamar irin su Injiniya Abdulsalam domin gyaran kasarmu Najeriya. Masu iya magana suka ce kowa yayi dakyau, zaiga dakyau. Ina mana fatan alheri.
Muhammad Bala Garba, (Alh Bawayo).