Udom Emmanuel Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabe Tare Da Kudirori Takwas.
DAN takarar Jam’iyyar PDP kuma Gwamnan da ke kan kujerar Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya kaddamar da takararsa domin ci gaba da darewa kan karamar mulkin na shekaru hudu a babban birnin Jihar da ke Uyo.ko
Tsananin yawan mutanen da suka taru awajen taron sun bayar da tsoro domin tsananin yawan magoya baya.
Gwamna Udom, wanda ya kasance cikin farin ciki da koshin lafiya ya tabbatar da cewa babu shakka zai sake lashe zabensa a karo na biyu,Inda ya tabbatar wa da jama’arsa cewa zai ci gaba da yi masu aiki domin samun romon Dimokuradiyya a daukacin sako da lungunan jihar.
Kamar yadda ya bayyana cewa ” Irin dimbin ayyukan da ya yi wa jama’ar Jihar su ne abubuwan da za su sa jama’a su ci gaba da ba shi dama a karo na biyu, kuma wannan zai faru ne da yardar Allah cikin ikonsa “ALLAH”
“Don haka zan ci gaba da yin ayyukan raya kara tare da riokn Gaskiya da Amana domin inganta rayuwar jama’a.
“Kwarewa ta a kan harkokin Banki da hada hadar kudi sun taimaka wajen samun cibiyar samar da ci gaba wanda ya taka rawa kwarai ta fuskar samun ingantacciyar hanyar ci gaban kasa musamman a bangaren tattalin arzikin jihar, misali na samu akalla shekaru Ashirin tare da Bankin Zenith, don haka kasancewa ta Gwamnan Akwa Ibom ya zamo wata kyauta ce daga Allah da ta zama rahama ga mutanen Jihar Akwa Ibom da Nijeriya baki daya.
“Kasancewa ta a cikin harkokin siyasa hakika ya tabbatar mini da cikar karin maganar da ake yi cewa “Hanyar Allah it ace mafi daukaka tare da samar da ingantaccen haske mai walkiya, walkiya domin samun rana mai cike da nasara”.
“ina son bayyana wa jama’a cewa zan ci gaba da samar da ingantaccen tsarin yin taka tsantsan a kan harkokin kudin Jihar Akwa Ibom har tsawon wadansu shekaru hudu masu zuwa, Gwamnan ya shaidawa magoya bayansa da suka hallara a wurin taron da ke Filin wasa na birnin Uyo.
Udom ya kuma bayyana manufar Gwamnatinsa guda Takwas da suka hadar da ci gaba da farfado da tsarin sufurin Jirgin sama, ayyukan raya kasa a kowane fannin bunkasa rayuwar Dan Adam, kara inganta fasahar sadarwa, aikin Gona,samar da masana’antu a kokarinsa na mayar da Jihar cibiyar masana’antu da sauransu
Manufar Gwamna Udom sun hadar da samar da ayyuka domin samun arziki, yin harkar siyara tare da kowa ba tare da Nuna wani bambanci ba Ko kadan.