Shaguna Hamsin Sun Kone A Kasuwar Kakuri Kaduna

0

Shaguna Hamsin Sun Kone A Kasuwar Kakuri Kaduna


A kalla rumfunan Hamsin ne suka Kone kurmus a kasuwar Kakuri da ke cikin garin kaduna a yankin karamar hukumar Kaduna ta Kudu a ranar Asabar da ta gabata.

Kamar yadda wakilinmu Imrana Abdullahi ya samu labari wanda daga bisani yaje domin ganewa idanunsa yaga irin yadda yankin da ake sayar da kayan abinci ya kama da wutar lamarin da ya haifar da asarar Kudi na miliyoyin Naira, yayanin Gobarar ya yi sanadiyyar samun damuwar wasu daga cikin yan kasuwar abin da ya haifar wa da wasu faduwa nan take wanda a yanzu suna kan gadon asibiti.

Majiyar ta kara da cewa wasu daga cikin yan kasuwar sun samu labarin faruwar lamarin ne cikin Daren Juma’ar da ta gabata.

Wani Dan Kasuwa Mai suna Malam Ali ya shaida wa wakilinmu cewa Shaginansa guda uku da yake bayar da sarin Lemun kwalba da sauran kayan abubuwan masarufi duk sun kama da wuta.

Duk da cewa ya zuwa lokacin hada wannan labarin ba a samu tantance abin da ya haifar da Gobarar ba, Amma daman wannan Kasuwa can a baya Tasha fama da matsalar Gobara irin wannan da ke haifar da asarar miliyoyin Naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here