Za A Hana Daukar Bakin Haure Aikin Gadi A Nijeriya – Gana

0

Za A Hana Daukar Bakin Haure Aikin Gadi A Nijeriya – Gana

Shugaban hukumar tsaron garin kaya ta (Civil Defence) ta kasa Abdullahi Gana Muhammad, ya bayyana cewa nan gaba daya za a yi dokar da za ta haramtawa bakin Haure yin ayyukan Gadi a duk fadin Nijeriya Baki Daya.

Abdullahi Gana ya bayyana hakan ne a garin Kaduna lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Gana, ya ci gaba da cewa tuni aka gano cewa Mafi yawan bakin hauren da ake ba aikin gadi a wadansu muhimman wurare da unguwannin masu hannu da shuni ana hada Kai da su ne a aikata ayyukan ta’addanci da ayyukan da suke kawo matsaloli ga harkokin tsaro.

Don haka nan gaba kadan za a yi dokar da za ta hana ire iren wadancan bakin Haure aikin gadi, wanda hakan zai bayar da dama ga kamfanonin tsaro su yi rajista kuma su samu damar daukar wadanda za su yi ayyukan a duk fadin kasa baki daya.

Indai za a iya tunawa aikin gadi musamman a unguwannin masu hannu da shuni tuni ya koma hannun bakin Haure musamman Buzayen fa ake kira Sadaka Yalla da wasu ke kira Jajaye Ko Bakaken Buzayen, da a wani kaulin ake cewa ana biyansu hakkinsu na yin gadi a duk sati sati Ko sati biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here