SAURA KIRIS DA AN SACE WAYAR HADIZA BALA USMAN

0

SAURA KIRIS DA AN SACE WAYAR HADIZA BALA USMAN


Daga Taskar labarai
Wani abin Al ajabin da ya faru a taron yakin neman zaben shugaban kasa Buhari da ya faru a kaduna a ranar jummar da ta gabata shine ..yadda wani Barawo ya kusa sace wayar Hannu ta shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya..hajia Hadiza Bala Usman.
Duk kuwa da cewa .tana cikin sahun Inda manyan baki suke a zaune .wadanda aka fi baiwa” kariya da taro .hasali ma Inda take zaune da Inda shugaban kasa Buhari yake zaune Babu nisa..Wanda akwai matakan tsaro masu tsauri a wajen
Amma Barawon har ya iya dauke wayar ta Hadiaza Bala ya Mika ma wani abokin satar shi..da suka shirya makidar a tare. Sannan aka Kama su
Majiya Mai tushe ta shaidawa Taskar labarai faruwar lamarin da kuma yadda ake mamakin ..yadda barayin suka iya ratsa duk shingen tsaron..Don yin satar..
Majiyar tace ga Alama barayin ba wayar Hadiza suka nufa ba..illa kila su samu wayar Don fitar da bayanan dake a cikinta..wadanda suka Shafi sakon Ni da sauran bayanai..
Majiyarmu ta Taskar labarai tace..barayin suna a hannun Jami an tsaro suna amsa tambayoyi…
Taskar labarai tayi kokarin Jin ta bakin hukumar Yan sanda ta jahar kaduna abin yaci tura..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here