AN BIYA KUDIN FANSA NA KOC DIN KWALLO NA KATSINA UNITED
Daga Taskar labarai
Wata majiya Mai tushe ta tabbatar wa da jaridar Taskar labarai cewa Alhaji Aminu Balele kurfi Wanda aka Sani da Dan arewa..ya biya diyyar kudin fansa na koc din kulub din kwallon kafa na Katsina united Wanda masu satar mutane suka dauke sati biyu da suka wuce.
Majiyar ..wadda Babba ce.a ma aikatar wasanni ta jahar katsina.ta ce Aminu Dan arewa shine Wanda ya Rika tattaunawa da barayin har aka cimma matsaya.kuma a lokacin da yake magana da Taskar labarai yace a iya saninsa an biya kudin saura a sako shi ko kuma an sako shi..yace ya saurari duk musayar tattaunawa da akayi tsakanin wanda ya Rika Shiga tsakanin ..Wanda aka nada a waya..
Shi dai koc din Mai suna Abdullahi Biffo .yayi sati biyu da dauka ana ta tattaunawa da masu garkuwa aka kuma bar abin shiru kar a Yaya ta…su tsawwala farashin.
A wani lamarin kuma makamancin wannan. P.a na galadiman Katsina Wanda barayi suka tafi dashi a motar galadima.har yanzu ba a dai dai ta dasu ba, wata kafa tace Mana ..sukan bugo waya su kashe wayar, in an danyi magana dasu..
___________________________________________
Taskar labarai cikakkiyar jarida ce dake Bisa Yanar gizo www.taskarlabarai.com da kuma shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter instigram da you tube.