An Kaddamar Da Kasuwar Baje Kolin Kayan Mata A Kaduna

0

An Kaddamar Da Kasuwar Baje Kolin Kayan Mata A Kaduna

kokarin da Iyaye mata ke yi domin amsa kiraye kirayen da Gwamnatin tarayyar Nijeriya karkashin Muhammadu Buhari na Mata da matasa su kama sana’o’i domin dogaro da Kansu yasa kungiyar gamayyar mata sama da Dari a kaduna suka dukufa wajen kere keren kaya dabandaban.

Za dai ayi wannan baje Kolin ne na tsawon kwanaki uku a filin Gidan ajiye kayan tarihi da ke kaduna da ke unguwar sarki kaduna.

Shugabar kungiyar gamayyar Matan ta kasa masu yin kayayyaki a Nijeriya Hajiya A’isha Gambo ta bayyana cewa babban dalilin da yasa suka fito da wannan Shirin shi ne domin fadakar da Mata kuma duniya ta san irin abubuwan da suke yi daga cikin garin kaduna da kewaye.

Wannan kokarin kasuwar baje Kolin Kayan kayayyakin an bude shi ne a filin Gidan Adana kayan tarihi da ke kaduna, taron ya kuma samu halartar muhimman mutane masana harkokin kasuwanci.

A’isha Gambo, ta ci gaba da cewa sun dauki matakin samun wannan gagarumar kungiyar mata masu kirkire kirkire ne domin Matan su samu damar a dama da su a cikin harkokin kasuwanci musamman a fagen irin yadda masana’antun mata suke a jihar kaduna.

“Da akwai wadansu matan da sun iya yin kaya Amma ba su san yadda za su fito a Sansu ba, wadansu kuma sun san yadda za su fito a Sansu Amma kuma ba su iya sana’ar ba don haka muka hada kan mata ta yadda za a samu ci gaban da kowa ke bukata”.

Hajiya Gambo ta kara da cewa akwai matan da suke Noma a cikin gidansu wasu kuma sun mayar da dakunansu wuraren koyawa mata sana’a wasu kuma suna yin kiwon Kifi a cikin gidajensu suna kuma kaiwa wuraren sayarwa dabandaban, domin a yanzu wasu matan za su sa hannu nan take su kama Maka Kifi.
Ta kara da cewa wannan taron farko ne nan gaba kuma zamu yi taron sallah domin mata su sayar da kayan da suke samar.

“Manufar mu ita ce a rika fitar da kayan da matan nan ke yi har zuwa kasashen waje, ta yadda za a mance da zuwa Dubai da wasu kasashen da yan Nijeriya ke zuwa Sayo kaya”.

“Mun kuma samu rumfar da zamu ajiye kayanmu a babbar kasuwar kaduna domin a rika sayar da kayan da aka samar”.

Hajiya Hajara Ahmad da take tofa albarkacin bakinta cewa ta yi sun shirya wannan taron baje Kolin ne domin fadakar da Mata irin manufar Gwamnatin Baba BUHARI na kowa ya tashi domin samun tsayawa da kafarsa

“Muna son mata su fadaka su gane me ake nufi da dogaro da Kai, shi yasa muka ce mata su fito kada a zauna haka kawai domin rayuwar yau Sai mace ta bayar da tallafi”. Inji Hajara.

“Kai har mata manoma Muna da su a cikin wannan kungiya ta mata, kaga ni kaina ina da Gona”.

Ta kuma yi godiya ga dukkan mutanen da suka taimaka wajen ganin wannan taron baje Kolin Kayan da mata ke samar wa ya samu nasara domin da kudin mu muke ta wannan fadi tashi.

“Kuma nan gaba zamu ta Fi har wajen shugaban kasa domin a samu fa’idar lamarin kasancewar mata sun tashi tsaye suna yin abubuwa kala kala”.

Kadan Daga cikin irin abubuwan da matan ke yi sun hada da Takalma,Jakunkunan Mata, Hulunan Yara da na manya, kayan kwalliyar Daki da na gida baki daya.
Akwai kuma wadansu kamfanonin matan da suka yi kayan abinci da abin sha da suka hadar da Zobo da Ganyen Shayi da aka yi a cikin fakiti fakitin zamani dabandaban Gwanin ban sha’awa.

Kadan Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Fasto Yohanna YD Buru, Alhaji Musa Gashash wanda ya gabatar da kasida a wurin taron a kan kasuwanci da yadda za a samu a wannan fanni, da kuma sauran manyan baki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here