MAHARA SUN ADDABI KAUYUKAN BATSARI DA SAFANA
Daga Taskar Labarai
A yau wasu mahara sun Kai farmaki wani gari dake da iyaka da safana da batsari..Mai suna salihawar daji Inda suka kashe wani magidanci suka tafi da kanensa da kuma dan sa…
Mai ba Taskar labarai bayani yace maharan sunzo suna tambayar wani gida ..Wanda suke Tambaya yaki Basu hadin Kai sai kawai suka kashe shi..suka kuma tafi da kanensa da kuma Dansa.
Wasu maharan sun kuma Kai Hari a Garin Tankuri cikin yankin na batsari Nan ma sun kashe mutum Daya suka tafi da mutane biyu kamar yadda wakilan Taskar labarai na yankin suka tabbatar
A shekaran jiya wasu maharan sun sace wani wani mutum a wani gari kusa da batsari..mutane suka bi maharan suka kwato mutumnin suka kashe maharan guda biyu.
Wakilan Taskar labarai suka ce Nan a. Makabartar batsari aka turbude maharan a wani Rami Daya da aka Gina Don kar a bar su..waje suyi wari
Duk da an rufe su..mutane saboda fushi sai su Rika zuwa kabarin suna Tofa masu miyau da Yi masu tofin Allah tsine.wasu ma har jifar kabarin suke..
Taskar labarai ta gano mutanen garuruwan sun fara hassala..Wanda sun fara daukar matakai Akan kansu.in sunji karar babur da dare sai su tashi su tare Don kare kansu da kansu.
Wannan ya Sanya barayin mutanen suka chanza salo.sai su ajiye baburansu ..nesa su tako a kasa.zuwa Inda suke son yin barnar su..in sun Kama Wanda suke son tafiya dashi sai su tafi dashi a kasa..har zuwa Inda suka ajiye baburansu..
Taskar labarai ta gano a satin nan kacal mahara sun Kai Hari da yawa a yankunan batsari, jibiya, safan, da wasu yankunan faskari da dandume..na jahar Katsina.