RUMFAR DATA RUMTA KAN MAGOYA BAYAN BUHARI A MAIDUGURI.

0

RUMFAR DATA RUMTA KAN MAGOYA BAYAN BUHARI A MAIDUGURI.

Muhammad Bala Garba, Maiduguri.

A ranar litinin 21 ga wannan watar ta January Shugaba Muhammad Buhari yaje Birnin Maiduguri domin gudanar da yakin kamfen din sa na wa’adi na biyu.

Shugaban ya isa jihar ne da misalin karfe goma sha daya na rana, daga filin sauka da tashi na jiragen Maiduguri ya wuce fadar mai martaba Shehu Barno suka gaisa, daga nan ya wuce filin motsa jini na Ramat square inda al’ummar jihar sukayi katutu suna jiran isowar sa.

Bayan shugaban ya iso filin ana tsakiyar gabatar da taro a daidai lokacin daya tashi don gabatar da jawabi wata rumfa ta rumta kan Jama’a.

See also  FG delivers relief items to over 1,000 flood victims in Katsina State

Rumfar ta ruguzo ne sakamakon hawa saman rumfar da wasu mutane suka yi domin su samu damar hango shugaba Buhari a yayin da ya tashi yin jawabi a wurin taron.

Mutune arba’in da takwas ne suka jinkata a dalilin batuwar rumfar, yayin da mutum guda ya rasu.

Daga Muhammad Bala Garba, Maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here