YAKUBU LADO MAYAUDARI NE…INJI SANATA AHMAD BABBA KAITA

0

YAKUBU LADO MAYAUDARI NE…INJI SANATA AHMAD BABBA KAITA

Daga Taskar Labarai

Sanata mai wakiltar Daura Alhaji Ahmad babba kaita.ya shelanta wa duniya cewa dan takarar gwamnan katsina a jam iyyar PDP Alhaji yakubu lado dan marke..mayaudari wanda a rayuwarsa ba abinda ya sani sai yaudara.
Sanatan yana magana ne a yakin neman zaben da jam iyyar APC tayi yau a garin mani.karamar hukumar mani
Sanata Babba yace, yaudarar sanata yakubu lado dan marke ba boyayya bace kowa ya san haka kuma ya san wannan.ya sha yima yan siyasa alkawali da kuma yima jama a. Alkawali amma ba ya cikawa.
Ahmad babba kaita ya kara da cewa .da naje majalisa na sanya an dauko mani fayil nashi wanda dana duba ba bu komai a cikin ..ko bihim bai taba tashi yace ba..sai ma halinsa da ya saba ya cigaba da yi
Ahmad babba ya kara da cewa, wannan dan takara ya taba cinikin zabensa ya saida ya kuma amshi kudin .ana sauran awowi a fara jefa kuri a…
Daga nan sanata Ahmad babba ya daga murya yayi tambaya da karfi..ko zaku zabi mayaudari ya zamar maku gwamna?
Jama a suka amsa da karfi…a.a.
Lokacin da aka ce najeriya duk filin ya dauka sai buhari da akace jahar katsina sai akace sai masari..duk aka amsa.mun yarda
Amma ana cewa dan majalisar tarayya sai wasu suka ce Bamayi..da akace mani sai muduru wasu ma sai sukace BAMAYI…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here