MAHARA SUN KAI WA YAN SANDA HARI A BATSARI!!

0

MAHARA SUN KAI WA YAN SANDA HARI A BATSARI!!
Daga Taskar labarai
A jiya da dare ne, ake Zargin wasu mahara da ake tsammanin masu satar mutane ne..sun Kai ma wani matsayar Yan sanda Hari dake wani Gari Mai suna shekiwa.wanda ke kilomita goma Sha biyar daga Garin batsari .. kilomita biyar daga Garin Ruma.
Wakilan Taskar labarai sunje wajen da abin ya faru da jijjifin safiyar yau litinin.inda suka ga barnar da. Maharan suka aikata.
Wakilan Taskar labarai sun tabbatar .wurin .waje ne da Yan sanda ke zaune Don gudanar da aikinsu na bada tsaro da kariya.ga jama a .
Ana zargin cewa ..maharan sun mamayi ..Yan sandan ne..Inda suka afka masu..ba zata. Kuma sukayi barna sosai har da jikkatawa..da Kona. Mota .kamar yadda wakilan Taskar labarai suka gani..da suka je wajen da abin ya faru..
Mazauna yankin sunce …sunji Karar bindiga da fitar harsasai Babu kakkaftawa..da dare .kuma Harbin ya Dade ..Yana fita ..daga Nan sai suka ga wuta na tashi da hayaki ya turnike sama .
Jaridar Taskar labarai tayi kokarin Jin ta bakin kakakin Yan sanda .na jaha..ya dauki wayar Amma ya shaida Mana cewa Yana a cikin mitin Don Haka ba zai iya magana ba…
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista dake Bisa Yanar gizo.www.taskarlabarai.com da kuma sashen sada zumunta na Facebook, Twitter, instigram, da you tube.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here