DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar PDP Honarabul Isah Muhammad Ashiru Ya kara fadakar da magoya bayansa a karamar hukumar Jaba a kan su kara jajircewa domin kawar da tsoro da kuma duk wata barazana lokacin zaben shekarar 2019 Mai zuwa.

0

DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar PDP Honarabul Isah Muhammad Ashiru Ya kara fadakar da magoya bayansa a karamar hukumar Jaba a kan su kara jajircewa domin kawar da tsoro da kuma duk wata barazana lokacin zaben shekarar 2019 Mai zuwa.

Da yake yi wa dimbin magoya bayansa a karamar hukumar Jaba ya ja hankalinsu game da batun siyasar Kudi da duk wata barazana da wasu Ko wani zai kokarin yi masu daga kowane jam’iyya Ko Dan takara da nufin yin magudin zabe.

Ya Tabbatar masu cewa idan sun jajirce hakika za su samu ribar wannan aikin.

Da yake jawabi ga dimbin magoya baya a Koi da ke karamar hukumar Jaba ya jawo hankulan mahalarta taron cewa jam’iyyar APC a Jihar Kaduna bata da wani abin da za ta iya tabuka masu a Jaba da Jihar baki daya inji Ashiru.

Ya ci gaba da cewa naji su suna cewa ” Koda kun zabi PDP, ba shakka kuri’arku ba wani Abu bace, saboda a karshe kuri’ar za ta zama mara amfani”, inji shi, Bari in gaya maku duk suna son yin amfani da farfaganda ne kawai.Amma ba su da abin da za su yi maku.

” Suna son keda maku tsoro ne kawai da shakku a cikin zukatan Ku domin kada Ku fito jefa kuri’arku domin kada Ku kawo canjin da zai taimaka wajen kawar da shugabanci da ake yi a Jihar Kaduna da kuma a kasa inda yan Nijeriya suke ganin tasku a karkashin jagorancin APC,”ya shaidawa dimbin jama’ar da suka halarci gangamin.

” Kada Ku Bari a tsoratar da ku, domin nasara a Gare mu take wanda Ko abokai nan hamayyarmu sun san hakan”, yana gaya wa dimbin magoya bayan da suke gamsuwa da bayaninsa

“Mafita game da wannan lamari yaku jama’a Ku sani Abu ne Mai sauki, Ku fito Ku kada kuri’unku, Ku kasa ku tsare Ku jira kuma ku tabbata an kirga ta sosai dalla dalla, Ku tabbatar kun samu cikakkiyar shaida daga nan Ku raka kuri’ar har zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe.

“PDP bata da kudin da za ta Baku cin hanci domin Ku zabe mu”, inji shi, “Amma manufar mu domin ciccibar Jihar Kaduna tare da Jama’ar ta zuwa Tudun mun tsira daga halin da take ciki”. Ya fayyace.

A jawabin Wanda suke yin takarar tare a matsayin mataimaki Honarabul Sunday Marshall Katung, wanda Shima ya yi wa dimbin magoya bayansa jawabi ya ce “APC a halin yanzu tana kokarin jan hankalinku da abin da take kira kudin yin kasuwanci Ko sana’a”, Inji shi.

“Wannan kudin cin hanci ne, kuma hakan yana faruwar ne alama ce ta rashin soyayya da rashin Ko in kula game da halin da jama’a suke ciki tun da suka zo kan karagar Mulki”.

“Ku yi hankali da irin wannan lamari na mutumin da ya jefa ka cikin wani Hali da safe Amma kuma da yamma ya ce Maka wai yana kaunarka domin kawai yana ganin kana da wata damar da shi yake bukata,”Ya ce.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jiha Cif Felix Hassan Hyat, ya gaya wa mahalarta taron cewa yana matukar garin ciki da irin yadda mutanen karamar hukumar Jaba suka kare kuri’unsu a lokacin zaben kananan hukumomi.

Ya ci gaba da cewa APC ba za ta iya yin magudi ba kuma su kira shi sahihin zabe sannan kuma su nada shugaban kwamitin rikon da zai shugabanci karamar hukumar.

PDP bata Ko shakka cewa Karamar hukumar Jaba za su ba PDP ne kuri’arku baki daya in kun Bada kuma ku tsare ta”, inji shi.

Taron dai ya samu halartar dimbin jama’a manya da sauran matsakaita baki daya da suka hadar da tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna Ambasada NUHU Bajoga,Tsohon shugaban kwamitin kula da harkokin wasanni na majalisar tarayya Honarabul Godfrey Gaiya,wadanda dukkan su yan asalin karamar hukumar Jaba ne.

Gangamin ya ci gaba inda Jirgin ya nufi zuwa karamar hukumar Sanga da Kaura su dai wadannan kananan hukumomi na karkashin mulkin PDP ne tun dawowar Dimokuradiyya a shekarar 1999.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here