MAHARA SUN KAME GARURUWA BIYAR A KATSINA

0

MAHARA SUN KAME GARURUWA BIYAR A KATSINA

Daga Taskar labarai

Wakilan Taskar labarai na musamman sun ruwaito cewa mahara masu fashi da makamai da kuma satar mutane don amsar kudin fansa, sun amshi wasu garuruwa biyar a karamar hukumar faskari ta jahar Katsina.

Taskar labarai ta tabbatar cewa garuruwan sune unguwar Tsamiya, Birnin Kogo, Raba, Zuru, da Unguwar Doka. Duk a karamar hukumar Faskari kan iyaka da jahar Zamfara da kuma karamar hukumar Dandume.

Taskar labarai ta jiwo cewa maharan sun zo sun shaida wa mutanen garin cewa wadannan garuruwan yanzu nasu ne, suke da iko dasu, sune za su rika bada umurni a cikin su, don haka duk wani mai fada aji daga wajensu zai rika amsar umurni.

Su kuma ba zasu sake taba kowa a garin ba. Ko kawo Hari a garin ko dan garin, ba kuma satar kowa daga garin duk wani dan garin yana cikin aminci nasu.

Wakilan​ Taskar labarai suka ce maharan sun kafa wasu tutoci wadanda aka yi da farin kyalle da ratsin Jan fenti.

Maharan sun fada wa ‘Yan garin cewa, za su rika sanar dasu duk wata bakuwar fuska ko wani shiri da aka iya yi a kan su.

Wani dake zaune a daya daga cikin garuruwan ya shaida wa Taskar labarai cewa, suna rayuwa cikin tsoro don mutanen basu da tabbas suna zuwa su yi yawo da makamai a gaban kowa ba wanda ya isa yace masu kanzil.

See also  FG Inaugurates Road, Gully Erosion Intervention Project At UNIBEN

Yace da sun ga bakon Ido ya shigo garin sai su yi ta waya suna tambayar waya shigo? Me ya kawo shi? Su kuma rika gargadi kar fa a saba yarjejeniya in aka Saba duk abin da ya biyo baya ruwan ‘yan garin.

Yankin Faskari ta jahar Katsina na daga cikin in da suke shan wahalar wadannan mahara sama da mutane hamsin na ‘yan wannan yankin na wajen masu satar mutane a daji. Cikin su harda matar wani manomi Alhaji Lado Mairuwa wanda matarsa da ya ya yansa biyu duk suna a wajen mahara.

Ko a cikin satin nan sun je Garin sabon Layi Galadima su ka tafi da mutane goma, akwai kuma wanda aka amso amma suka dawo suka ce kashe shi suka zo yi kuma suka kashe shi.
Yankin ya zama kowa cikin tsoro da firgitarwa yake rayuwa.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista dake bisa Yanar gizo www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, Instigram, da youtube da whtsaapp a lamba ta 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here