MAHARA SUN KAI HARI GARIN YANKARA . FASKARI JAHAR KATSINA

0

MAHARA SUN KAI HARI GARIN YANKARA . FASKARI JAHAR KATSINA
Daga Taskar labarai
Wasu mahara sun Kai Hari a Garin yankara ta karamar hukumar Faskari..jahar Katsina ajiya da dare.inda har suka tafi da wata yarinya Budurwa.
Wakilan Taskar labarai da suka Isa Garin na yankara da jijjifin safiyar yau.Alhamis 31/1/2019.sun ga mutane na tsintar kwafsan alburasai yashe a kasa, Wanda maharan sukayi ta harbawa
Yan Garin sun fada wa wakilan Taskar labarai cewa .maharan sunzo wajen karfe Sha Daya na dare suka rarraba kansu Inda suka datse duk wata hanyar Shiga da fita Garin ..sannan suka fara harbi Babu kakkaftawa kuma sun dau tsawon lokaci kafin su bar garin
Yan Garin sun fadawa Taskar labarai cewa ..daga nan suka fara bin wasu gidaje ..Kai tsaye suka nufi gidan wani inyamuri Dan kasuwa ..Wanda yake sananne. A Garin .
Taskar labarai ..taga yadda maharan sukayi harbi kofar gidan inyamurin da bindigogi…Wanda kamar yadda zaku gani a hoton da jaridar ta dauka na gidan Wanda ke hade da wannan rahoton..
Da kyar suka iya Shiga gidan suka iske bayanan sai matarsa da kanwar matarsa.inda maharan suka barwa matar sako suka Kama kanwar suka tafi da ita kamar yadda aka tabbatar wa wakilan Taskar labarai a kofar gidan inyamurin da aka Kai harin.
Daga baya Jami an tsaro sun Kai dauki .Wanda maharan naji soja sun nufo Garin Daga wani karamin mazaunin su da ke kusa da Garin na yankara sai maharan suka bar Garin cikin gaggawa.
Maharan sun zo ne a Bisa babura.da goyo uku uku wasu hudu ..Wanda yankin na faskari sun Saba ganinsu da iri,n wannan Shiga da an gansu kowa sai yayi ta kansa.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce da ke da cikakkiyar rijista dake Bisa Yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook Twitter instigram da you tube.da whazzapp ta lamba 07043777779 .kwararrun Yan jarida ke gudanar da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here