Yan Mata Uku ‘Yan Gida Ɗaya Sun Mutu Bayan Kwanciyar Bacci.

0

‘Yan Mata Uku ‘Yan Gida Ɗaya Sun Mutu Bayan Kwanciyar Bacci.

======================================

Al’ummar Unguwar Badawa da ke yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano sun tashi yau asabar da samun labarin mutuwar wasu ‘yan mata guda uku a cikin dakin kwanan su.

‘Yan Matan uku, da suka hada da Walida mai shekaru 20 da Zuhaihatu mai shekaru 19 da kuma Wasila mai shekaru 11, ‘yaya ne ga Alhaji Salisu, kuma dukkaninsu sun rigamu gidan gaskiya a cikin barcin su.

Mahaifin ‘yan matan uku Alhaji Salisu, wanda ke cikin halin ɗimuwa ya kasa cewa uffan ga manema labarai, to amma Alhaji Habibu Muhammad Dan’uwa gare shi ya bayyana cewa kawo yanzu ba’a kai ga gano ainihin abin da ya zama ajalinsu ba, an dai tashi kawai da safiyar yau an ga gawarwakin su uku jere.

See also  Gwamna Radda ya gana da kamfanonin kwararri kan samar da kudaden shiga, zai gayyato su don bunkasa tattalin arzikin jihar

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, kuma ya ce zasu gudanar da bincike.

Tuni dai aka mika gawarwakin ga hannun kwararru domin gano musabbabin mutuwar su, kuma aka mayar da su gida aka yi musu sallar Jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here