Masu satar mutane don amsar kudin fansa sun sace matar Alhaji miftahu yakubu ciro dan musa.
wadda aka sace mai suna Hajiya Amina.
Ita dai hajiya Amina bello diya ce ga dan majalisar jaha Alhaji Bello Abdul wahab
Taskar labarai ta jiyo cewa barayin sunzo ne bisa babura da daren ranar lahadi wayewar garin litinin 4/2/2019 suka zo gidanta a tsakiyar garin danmusa.suka tafi da ita. A lokacin da suka zo ..maigidanta baya a gida.
An ce barayin sun so tafiya da wata mai waina mai suna Baba mai mai waina da suka gagara daukar ta .duk sai suka yanka mata hannaye suka bar ta.