TAWAGAR BARKIYA SUN SHA DA KAR A KAITA

0

TAWAGAR BARKIYA SUN SHA DA KAR A KAITA

Daga Taskar labarai:

Tawagar dan takarar sanata katsina ta tsakiya Alhaji kabir Barkiya na jam iyyar APC .Sun sha da kyar a garin kaita ta karamar hukumar kaita
Taskar labarai taga wasu motocin da aka farfasa wa gilashi.wasu kuma a akayi masu rotse a jikinsu.yayin da wasu motocin suka sha da kyar
Wakilan taskar labarai sunga wasu da suka tsero daga garin inda suka biyo ta gonaki don cetar ransu
Wani da a akayi abin a gabansa ya shaida wa taskar labarai cewa tunda suka shigo garin akayi masa sallama da ihu da ruwan dutsu har zuwa fadar mai daraja sarkin kaita a fadar ne ..barkiya na ciki har sarkin ya bashi kyautar sarauta.sai jifan da bugun motoci da itatuwa ya kazanta.
Mai ba taskar labarai yace da kunnensa yaji dan takarar sanata kabir barkiya na ta addua tun yana yi boye .har bai sani ba ta rika addu ar a bayyane kowa naji.
Taskar labarai ta bincika me ya kawo jifar? Wasu sun ce fushi ne matasan garin ke nunawa akan an fitar da daukar ma aikatan zabe da za a dauka amma babu yan kaita da yawa
Masu wannan ra ayin sunce har jami in hukumar zabe na kaita suka so su buga don nuna hushin nasu.
Wasu kuma sunce a a jam iyyar APC dashi dan takarar na sanata akayi wa wannan boren.sunce ko lokacin zuwan gwamna yakin neman zabe an so ayi wannnan tawayen amma manyan gari suka taushi mutane
Dan takarar dai ya fita garin na kaita lafiya amma ba tare da yin lacca zabe ba ,kamar yadda aka sabayi ko ina
A zaben da za ayi nan da kwanaki sha daya.daga cikin yan takarar da APC ta tsaida marasa farin jini akwai sanata na katsina da kuma na funtua kamar yadda binciken taskar labarai ya tabbatar
A katsina yiyuwar faduwar dan takarar tafi rinjaye .fiye. da tabbacin nasararsa..kamar yadda wasu nazari takwas da taskar labarai ta gano a zayyane
Daga cikinsu wanda taskar labarai take da tabbas shine duk garinsu kabir barkiya..watau kauyen barkiya bai taba samar wa kowa aikin gwamnati ba.koda kuwa sharar titi ne..da wasu hujjojin.
Amma dai ba san maci tuwo ba .sai miya ta kare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here