Badaqala A TETFund: BCO Ta Nemi EFCC Da DSS Su Cafko A.B Baffa

0

Badaqala A TETFund: BCO Ta Nemi EFCC Da DSS Su Cafko A.B Baffa

Daga Muhammad Abubakar

Qungiyar Kamfen Din Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, wato ‘Buhari Campaign Organization’ (BCO) ta yi kira ga Hukumomin EFCC da DSS da su cafko tsohon Shugaban Hukumar TETFund, Dakta A.B Baffa.

Qungiyar ta BCO ta yi wannan kira ne a jiya a wata takardar manema labarai da Daraktan Sadarwa da tsare-tsare, Mallam Ibrahim Gidado (Sarkin Yamma) ya sanya wa hannu.

Qungiyar BCO ta yi shelar cewa, akwai matuqar buqatar hukumar EFCC ta kama tsohon Sakataren, A.B Baffa ne saboda abubuwan ta’asa da ya aikata yayin da a ka ba shi amanar hukumar TETFund, inda ya yi amfani da wannan damar wurin cin amanar qasa da tarwatsa baitulmalin hukumar ba bisa qa’ida ba.

Takardar ta BCO ta bayyana cewa; “A qoqarin zabo nagartattun mutane wadanda a ka yi musu shaidar gaskiya da riqon amana ne ya sa Shugaban Qasa Muhammadu Buhari da Ministan Ilimi suka dauko Dakta A.B Baffa domin ya ja ragamar Hukumar Ilimi ta TETFund. Musamman ma don a samu daidaito, ci gaba da bunqasa a bangaren na ilimi.

“Kafin a dauko A.B Baffa sai da a ka yi la’akari da irin jajircewarsa a lokacin da yake shugabantar Qungiyar malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Bayero, Kano da kuma lokacin da ya jagoranci qungiyar ASUU din a matsayin shugaba na shiyya. Wannan ya sa a ka kyautatawa A.B Baffa zato da cewa, zai kawo ci gaban da gwamnatin Muhammadu Buhari ke fatan gani a fannin ilimi.

Haka kuma, Qungiyar ta BCO ta yi fashin baqi kan wasu daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsige Baffa a matsayin Sakataren Hukumar TETFund, inda ta bayyana cewa, ya wulaqanta kujerarsa da ofishinsa ta hanyoyi da dama.

See also  Ƴan sanda sun kama matar da ta bi sirikan ta har gida ta yi musu dukan tsiya

“Daga cikin dalilan tsige shi akwai batun daqile malamai masu qaro karatu a qasashen qetare. Inda ya yi ta muzanta su, tare da yi musu hawan qawara. Ya yi amfani da ofishinsa wurin musgunawa da yawan malaman da ke karatu a wasu qasashe, ta hanyar ayyana makarantunsu a matsayin wadanda basu dace a yi karatu a cikinsu ba.

“Haka kuma ba da yawun Gwamnatin Shugaba Buhari ba ne A.B Baffa ya kutsa kanshi cikin siyasa. Wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sa dole a bincike shi kan yadda ya tafiyar da dukiyar Hukumar ta TETFund. A kan wannan ne ma ya sa muke kira ga EFCC da ta cafko shi domin yi mishi tambayoyi.” Inji BCO

Qungiyar BCO ta kuma ce; “Ya kamata Hukumar DSS ta kama A.B Baffa ne bisa irin kalaman tunzarawa, bata suna da ya yi ta faman yi. Domin ba zai yiwu don Shugaban Qasa ya tsige shi ya koma yana yin yarfe ga gwamnati, da qoqarin tunzara al’umma. Duk kuwa da cewa, A.B Baffa ya kwana da sanin cewa, doka ta ba Shugaban Qasa dama ya tsige shi ko da kuwa bai aikata laifin komi ba. Alhali shi kwance yake dumu-dumu cikin laifuka, take haqqi, da almundahana, wanda malaman Jami’o’i sun fi kowa sanin haka.” Inji Qungiyar ta BCO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here