Kungiyar Darikar Tijjaniya ta amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dantakarar ta na shugaban kasa

0
538

Kungiyar Darikar Tijjaniya ta amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dantakarar ta na shugaban kasa a zaben ranar Asabar dake tafe.

Darikar Tijjaniyya ta kasa ta amince da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dantakarar ta na shugaban kasa a zaben gama gari da za’a gudanar ranar 16 ga watan Feburairu. Kungiyar ta hori mabiyanta dake fadin kasarnan da su zabi Shugaban kasa Buhari a duk inda suke.

Ahmed-Rufai Kakakin Darikar Tijjaniya wanda kuma shine Shugaban kungiyar nan ta SUFI (Stand Up For Integrity) movement of the Tijjanniya, ya tabbatar da cewar Darikar Tijjaniyya ta amince da sake zaben shugaban kasa Buhari a zaben shugaban kasa dake tafe na ranar 16 ga wannan wata.

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kungiyar Izala ta ayyana Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dantakarar ta na shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe.

Ahmed-Rufai yace kungiyar ta amince da Shugaban kasa Buhari ne tayin la’akari da yarda da kamun ludayin shi, hakan yasa suka yanke shawarar sake amincewa da zabar shi na tsawon wasu karin shekaru Hudu.

“Mun shaida Shi mutumin kirki ne kuma mai kishin kasa, ire-iren shi yanzu a Najeriya kadan ne a cikin Shugabannin da suka shude da kuma na yanzu.

Bayan zayyano muhimman cigaba da Najeriya ta samu karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannoni daban-daban na gida da ketare. Ahmed Rufai ya hori mabiya darikar Tijjaniya da sauran yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwata ranar zabe domin tabbatar da Shugaban kasa Buhari ya sake komawa karagar mulkin Najeriya karo na Biyu.

Bashir Ahmad (Mai taimaka wa Shugaba Buhari a bangaren yad’a labarai na zamani) 12-02-2019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here