MAHARA SUN KAI HARI BATSARI

0

MAHARA SUN KAI HARI BATSARI

daga Taskar Labarai

Wakilan jaridar taskar labarai sun isa garin kasai ta batsari.a karamar hukumar batsari..inda barayi suka yiwa garin kawanya a daren jiya asabar! 16/2/2019 sun bi gida gida suna kwasar dukiya.sun kuma harbi har mutane biyar. Sunyi awa uku cak suna tu annati
Jam in tsaro na soja sun kai dauki a inda maharan ke barna, amma maharan sukayi masu kwantar bauna…
Maharan sun saci dukiya a garin..
Wani dan garin ya fadawa wakilan mu cewa ..maharan sunzo da yawan gaske.sai suka raba kansu.mutanen garin sun fito suna kare kansu ta gabas..sai maharan suka biyo masu ta yamma..sun girke irin babbar bindigar nan mai aman har sasasai…suna kuma dauke da manyan makamai.
Maharan da suka ji karar motar soja na zuwa.sai sukayi masu kwantar bauna
Duk kokarin jin ta bakin kakakin watsa labarai yaci tura…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here