DAN MAJALISAR FUNTUA YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA
Daga Taskar labarai
Kwanakin baya ,saura kiris da Dan majalisar dokokin katsina daga karamar hukumar funtua, Abubakar Total,ya fada hannun masu satar mutane da suka tare hanyar sokoto ta zuwa garin jibiya.
Taskar labarai ta jiyo cewa Dan majalisar ya dawo daga sokoto ya biyo ta gurbi bai sani ba ,ashe mutanen na a hanya, sai kawai ya gansu a Gabanshi, gashi yana tuki a guje,ai sai kawai ya ki tsayawa su kuma suka bude wuta da bindigoginsu
Allah ya tsare basu same shi ba.ya wuce suka hahharbi motar,sai da ya kai wani waje motar ta tsaya.ya fito ya samu wata mota ya shaida masu cewa.ga abinda ke faruwa.suka dauke shi har zuwa wajen wadansu sojoji.
Dan majalisar mai suna Muhammad Abubakar total ya sha,amma anyi harbi motarsa sosai.