SANATA KATSINA TA TSAKIYA, WA ZAI KAI LABARI.? BARKIYA KO DAN LAWAN.?
Daga Taskar labarai
Wata kuri ar jin Ra ayin jama a.da jaridar taskar labarai ta yi a tsakanin kananan hukumomi guda tara na yankin mazabar sanata katsina ta tsakiya.kana nan hukumomin Kuwa sune .Katsina.Rimi.jibiya.kurfi.dutsinma.batsari.safana.dan Musa.batagarawa.
Jin Ra ayin ya kama kowace karamar hukuma aji Ra ayin mutane da tabbayar wa zaka zaba a matsayin sanata? Dan lawan ko barkiya.?
Kashi 70 cikin dari na wadanda aka zanta dasu,sai kaji sun ce DAN LAWAN. in aka tambaye su dalili sai kaji kowa na bayar da irin tasa hujjar
Wani abin da ya bada mamaki.hatta a karamar hukumar kurfi.ra ayin yayi kunnen doki tsakanin masu goyon bayan Dan lawan da ,kuma na barkiya.
A dutsinma kuwa .Sam Dan lawan ya zarce barkiya. A kaita.masu son barkiya sun fi na Dan lawan yawa.
A katsina kuma kunnen doki akayi.a cikin wadanda aka tambaya.a jibiya.duk Wanda ka taba sai kaji yace Dan lawan.
Jin ra ayin an dau kwanaki uku ana binshi
Amma gaskiyar hukunci masu zabe? Sai ranar asabar gaskiya Zata nuna.