SU WAYE KANTOMOMIN DAKE MA PDP AIKI? Gwamnatin katsina ta gano biyar

0

SU WAYE KANTOMOMIN DAKE MA PDP AIKI? Gwamnatin katsina ta gano biyar
Daga Taskar labarai
Gwamnatin katsina ta gano cewa a cikin kantomomin kananan hukumomi na katsina akwai wasu da suke da Alaka da yan PDP sunyi alakawali dasu akan in PDP taci Zabe za a saka masu.kuma ana zargin kudi suke amsa a wajen yan PDP
Su kuma suna baiwa mutanen na PDP duk bayanan sa suke bukata suna hada kai dasu a asirce.da anyi abu zasu Kwashe su fada masu.
Wannan lamari ya Sanya gwamnan na katsina a yau laraba ya Kira wani taro na gaggawa da kantomomin yayi masu ta tas..
Wasu kantomomin sun tabbatarwa da taskar labarai da zaman kuma suka ce gwamnan ya fusata ya kumayi masu magana cikin bacin rai.
Ya fada masu cewa ni abin arziki nayi maku .in kun saka mani da tsiya,Allah shine mai hukunci.
A zaman ance lallai an gano kantomomi biyar wadanda suke daukar bayanan gwamnati suna kaiwa PDP don haka ba zasu taba amincewa da wannan ba.
A zaman an ki bayyana ko su waye.sai dai bayan taron akayi ta gungu ana zunde da shafi fadi
Jaridar taskar labarai. ta watsa komarta don gano ko wadanda yan PDP ne a matsayin kantomomin APC?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here