Daular Tsar ta “yan Bolshevics

0
693

Tafiya mabudin ilmi

Daular Tsar ta “yan Bolshevics (2)

“Ka tuna 1939?” Pavel ya tambayeni, lokaci guda qwaqwalwata tayi wani irin zooming “lallai na tuna” nace da Pavel. Pavel yayi murmushi yace min _Lenin ko Stalin_ na yi murmushi nima na ce Vladmir Lenin yayi tsit haka, ya dan kalleni ni, na sadda kaina qasa muka cigaba da sauka qasan bene tare da baturiya daliba “Yar Russia Maria

Tun shigowata Birni na biyu a Russia (St Petesburg) daga Moscow na zaqu in jeni Hermitage Museum (Museum ta biyu a duk fadin duniyar nan) amma da yake munje a gajiye kuma kashegari da safe zamu hau jirgin sama zuwa birnin Volgograd don kallon wasan Nigeria da Iceland ga tsananin sanyi, ala tilas na kwanta na dan matse a dakina na hotel din Park Inn.

Dayake Hermitage Museum hanyoyin shigarta da qafa duk na qarqashin qasa ne (tunnels) dole sai da na samo city guide daga reception na hotel dina.

Na jeni Hermitage da wuri lokacin ma basu bude kofofin shiga ba, kuma da yake bangare bangare ne, ni dama nafi shaawar bangaren tarihin yaqin duniya na 2 ( Don za a iya cewa babu birnin da ya fi St Petesburg ganin masifar yaqin) shi yasa kusan ko a Jamus baza ka samu first hand artefacts na 2nd world war kaman yanda za ka samu a wannan birnin da nike ciki ba. A wannan birnin ne sojojin hitler na Nazi suka sauke bama bamai sama da milyan daya, a wannan birnin ne kadai a tsohuwar tarayyar soviet sojojin na 3rd reich suka kori Red Army na Tarayyar soviet din suka mamaye ilahirin birnin karakaf dinsa, suka dinga bi gida gida suna yanka maza da mata manya da yara. Bala’i kan bala’i, ka zauna a gida sojan Jamus ya shigo ya yanka ka ko bom ya fado ya qoneka, ko yunwa ta kashe ka. Uwa ta fito waje tsananin sanyi ya kashe ta, ance akwai gungun matan da suka fito nemawa yayansu koda ruwan sha ne (namaga hotonsu) suka nufi kogin Neva da ke wajen birnin da tulunan ruwa ana tsaka da yaqin, sun yarda ko su dawo ko su mutu, haka suka je har bakin kogin nan suna tsallaka gawarwaki da baraquzan gini, amma suka je suka tarar kogin ya daskare ya zama qanqara saboda tsananin sanyi ( An taba samun shekarar da shi wannan birnin ya dara ko ina a duniya tsananin sanyi, ance a anguwar Oyaniyakun na birnin an taba samun -67 wanda ba a taba samu ba a tarihin duniya)

Duk da sammakon zuwa da nayi, na iske qofar Hermitage cike da mutane (musamman irina, da arzikin qwallon world cup ya kawo mu) na zauna kusa da wasu dattawa miji da mata turawan mexico a jikin ginin mutun mutumin sojojin da suka yi nasarar qwato birnin, muna jiran a bude qofar (don an rubuta baza a bude qofar ba sai 11 na rana a bakin qofar)

Ina zaune bayan mun danyi hotuna da turawan Mexicon nan, haka sai na dan matsa harabar wurin abinka da Explorer ko zan tsinci wata ribar qafar na wani abin ganin kafin shigata cikin museum.

Na biyo ta wani dan dandamali mai furanni kala kala ina ta makyarkyatar sanyi, sai naji muryar mace a bayana “Are u a Nigerian?” (nayi mamaki jin kai tsaye an ambaci qasata duk da babu wani alami a jikina da ya nuna qasata) “Yes am a Nigerian” na amsa mata bayan na waiwayo

“I’m Maria, my russian name…. huh Mary in english” “Oh, i can see” na ce mata ina makyarkyatar sanyi, har haqorana na kaf kaf.

“Am a student of social anthropology from kiev university doing my thesis on devastating moral antics on leningrad during war” ta fada da eastern slang irin na scandinavian din nan, “You are from Oslo i suppose?” na tambayeta “Nope, am a russian” Abin da ya bani mamaki da ita gaskiya bata yi qirar mutanen russian ba, tafi kama da turawan norway a accent na slang dinta da appearance nata

A gurin budurwa Maria na qara samun bayanai masu tarin yawa har lokacin bude qofar hermitage museum, muka je muka yanki tikiti muka shiga, kudin tikitin shiga rubi 500 (kwatankwacin N5,000) sannan dai a ciki muka biya kudin tutor don muji dadin sharbar bayanai

Duk yanda kakai da qwaqwa baka isa ka iya gamawa da iya bangaren yaqi (armies) na gidan tarihin hermitage a kwana daya ko biyu ba, in dai ba tafiyar zuqu zakayi ba. A hermitage akwai artefacts na tarihi sama da milyan ukku, kowanne kuma akwai bayani a kansa.

Wato yanda na fuskanci mutanen nan, kaman yanda turawan ingilishi suka yi mana ne bayan sun cinye daular mu ta usmaniyya da yaqi suka sassace komi namu na tarihi, rubuce rubuce da fasahohin mu da muka gada iyaye da kakanni suka kai gidan tarihinsu na London, to hakama Rushiyawa suka sassace kusan ilahirin kayan tarihi na yaqin duniya na daya da na biyu da suke a Berlin da wasu yankuna na Poland da Czechoslovakia (ta lokacin) sakamakon sune kadai suka dangana har ga fadar hitler dake a berlin bayan sun cinye Jamus da yaqi.

Duniya bata taba ganin asarar rayuka da dukiya irin na yaqin duniya na biyu ba ana cewa sama da mutum milyan 20 aka rasa a yaqin na kusan shekara 12. Tun bayan ayyanawar yaqin da hitler ya yi, ya fadawa duniya yanason kafa “supreme reich” Daular Jamusawa burbushin kowacce al’umma, har ya fara da laqume maqwabtansa na kurkusa Viennan Austria da Czechoslovakia da taimakon Italy da Japan, wanda a lokacin manyan qasashen turai na Faransa da Ingila da ma sauran qasashen duniya suka yi gum da bakinsu suna daukar kaman rikici ne na gabashin turai su bai shafesu ba

Tutor dinmu mai suna Pavel ya tambayemu Tourist ne mu ko kuwa? Maria ta ce masa AA ita daliba ce yanzu haka, ni kuma nace nima tsohon dalibin history ne, kuma a qashin kaina na yi karatuttukan litattafai masu yawa akan Yaqin duniya na biyu da rawar da Russia ta taka wajen kubutar da duniya masifar hitler( duk da raayina akan hitler na gaskiya ba shi na fada masa ba) yayi murmushi shine ya tambayeni zan iya tuna 1939, nace masa qwarai kuwa, muna yi muna tafiya ta matattakalar benen qasa, (dayake bangaren da zamu a gidan qasa ne)

1939, shekarar da duniya ta fara jin qamshin tahowar bala’i, shekarar da makiyaya ko manoma (tun daga quryar yammacin Turai zuwa tsakiya zuwa gabashi) idan suna gona ko wajen dabbobinsu ko leburori a wajen ayyukansu, ko dalibai a ajujuwansu kai hattana mabarata a titunan turai kowa da kowa yasan mamayar da Jamus tayiwa Poland rana daya bayan ta mamaye wadancan qasashen yana alamta lallai Hitler ya gama shiri kuma da gaske yake yi yana shirin shigar da duniya musibar yaqi.

“Meyasa ka zabi Lenin akan Stalin” Pavel ya tambayeni, “Ni a gurina Lenin shine mai kishin Russia na gaskiya, na dade ina bin aqidun lenin tun daga kafa aqidar bolshevics da yayi da kuma duqufarsa ga kare mutunci da tattalin arzikin mutanensa, sabanin Stalin wanda kowa ya yarda azzalumi ne kuma mayaudari” na bashi amsa

“Amma Stalin ne ya kubutar da duniya ba ma Russia ba daga bala’in Hitler, sannan yayi nasarar kafa daular gurguzu a kusan ilahirin gabashin turai har da tsohuwar Jamus ta gabas” yace da ni

Na rigada nasan matasan russia na yanzu sun fi raayin Stalin saboda ya kawo masu irin sauyin yammacin turai na holewa sabanin wanda ya nemi dorasu akan gargajiyar da suka gada iyaye da kakkani, saboda haka nasan ma bata lokaci ne in tsaya gardama da Pavel a kan hakan, maimakon haka sai na canja akalar maganar “Mene ne gaskiyar maganar da ta fito daga bayan nan cewar Stalin ya taba zama da Hitler a asirce har sun yi yarjejeniyar ayaga na qasashen gabashin turai sannan ita kuma Poland zasu rabata biyu tsakaninsu amma daga baya Stalin din yaci amanar Hitler, wanda ya jawo Hitler ya fara tunanin mamaye Soviet din ma kanta?”

“Kana karanta qarairayin propaganda na western axis kenan?” inji Pavel “Inason gayamaka wani abu” ya cigaba “Ko da yarjejeniya ko babu Hitler ya yi niyyar mamaye Soviet. A tunaninsa tunda bashi da isashen filin noma, zai iya maishe da qasarmu gonakin nomansa” zan kuma gayamaka wani abun inji Pavel, ko Hitler ya mamaye mu ko bai mamayemu ba dama Stalin ya fara shirya masa, muma muna da tsarin mamayarsa” Pavel ya bani amsa ko ya sani ko bai sani ba

Na so ace zuwan mu Moscow zamu dade, amma matsalar masaukin Super Eagles na Nigeria a birnin St Petesburg ne (Mahaifar Shugaban Russia na yanzun Vladmir Putin), da mun jima a Moscow lallai da sai na kai ziyara Lenin Boulevard (Inda gawar marigayi Shugaban “yan gurguzu na duniya kuma tsohon shugaban tarayyar soviet Vladmir lenin take) har yanzu gangar jikin Lenin wanda ya rasu tun shekarar 1925 tana nan, ana sanya mata magani ne don kada ta rube. “Yan yawon bude ido da irina “yan ganin qwaqwaf basa yankewa a Lenin square don ganin gawar, duk da kuma akwai dokoki masu tarin yawa na shiga gurin, misali bayan an caje ka kafin ka shigan ba za a yarda ka shiga da irin hular nan hat ko ka shiga kana zuqar tabar sigari ko tabar lofe a farfajiyar inda gawar take ba, haka hatta hayaniya mai yawa ba za a yarda kayi ba duk don girmamawa ga Shugaba Vladmir Lenin.

Nayi karatuttuka masu zurfi akan rayuwar Lenin kusan tun bayan gama Makarantar Sakandire, Malaminmu na tarihi idan yana bamu darasi akan lenin har kaman yayi qwalla. Akan labarin lenin har sai da muka fara zana hotunan biranen Moscow, Kiev da St Petesburg a zuciyoyinmu, da yanda tsananin taqadarcin lenin din yasa aka dinga korarsa a makarantun da ya shishshiga, har lokacin da yaji labari akan titi ana neman wadanda zasu shiga kwas na law, ba tare da ya taba zama darasin law din ba ya je ya zauna a jarrabawar a Jami’a ya kuma cinye duk kwasa kwasan lokacin. Lenin na tsaka da jagaliyarsa ne yaci karo da shahararren littafin nan na Karl marx mai suna Das kapital karanta littafin da abubuwan da yaji wajen Marx sai ya bashi amsar yanda za a warware rikicin ma’aikata da Sugabanni da yaqi ci yaqi cinyewa a Daular Tsar ta lokacin, wannan ne kuma dalilin lenin din na fantsamawa cikin gwagwarmayar kafa daular gurguzu da yaqi da aqidar jari hujja. Bayan shan dauri kala kala da kora daga gida da qasa, har dai yayi nasarar kafa daular gurguzu kuma ya zama shugabanta

“Me yasa baka son Stalin” Maria ta tambayeni bayan sun dade suna maganganunsu da Pavel sun qyaleni ina ta tunano abubuwan da na sani game da Lenin “Ni a gurina Joseph Stalin bashi da maraba da Adolf Hitler dukkaninsu suka yi shiru, ni kuma dama so nike in yi masu fyadin “yan kadanya don su qyaleni da zancensa, “Joseph Stalin munafiki ne, tare suka shirya mamayar duniya shi da Hitler” na cigaba “sun yi meeting na yanda zasu yi ayaga ta qasashen gabashin turai tsakaninsu, har sun kasa lithuania,latvia,estonia, belarus, ukraine da finland tsakaninsu, sannan yaqin da Stalin ya yi da finland ya tona masa asiri har Hitler yake zaton ashe ma fanko ne, shiyasa ko da suka shiga Poland a tsakaninsu sati biyu rak, suka yi muguwar barna tare, irin cin zarafi na qona gidaje, fyadewa mata, da bautar da mutane a gidajensu wanda Nazi sukayi irinsa Red Army qarqashin Stalin suka yi, wanda ni da kai mun san in ace Lenin ne bazai yi haka ba. Stalin ne ya jagoranci mamaye Iran can a Gabas ta tsakiya sannan bayan qarewar yaqin 1945 a Tehran suka yi meeting shi da Churchil na Ingila da Roosevelt na Amurka suka kitsa kinibibin baiwa Yahudawan Sahyoniya yankin Palastinu”

Da haka dai har muka gangara cikin dakin tarihi na Hermitage

In Allah yaso a kashi na gaba zan kawo abubuwan mamaki da idona ya gane min a gidan tarihi na Hermitage

Sai mun hade

Naku
Dan umma
Hassan Dandy

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here