Wani bawan Allah ne ya bada ajiyar keken hawansa awani shagon siyar da kayan masarufi a kasuwar garin Zanajan a arewacin kasar Iran. Ya tafi bai dawo ba.
Mai shagon sai ya ajiye wannan keken a kofar shagonsa bisa sa ran dawowar wannan bawan Allah tsaho shekara 45.
Wata biyu da suka wuce sai wannan mai shagon ya rasu, shine hukumar garin ta sashi wani alami aka kuma ajiye keken a wajen saboda girmamawa.