YADDA AKA TAKURA YAN ADAWA ANA GAF DA ZABE…

0

YADDA AKA TAKURA YAN ADAWA ANA GAF DA ZABE….don kar su fitar da kudi
Daga Taskar labarai
Wani bincike da jaridar taskar labarai ta gano yadda hukumomi masu bincike na tattalin arziki suka tadama wasu da ake ganin suna da kudi zasu iya baiwa jam iyyun adawa da yan takarar su hankali.
Don su tsorata su,su hana su motsin fitar da kudade a lokacin zaben!.
Bincike na taskar labarai ya tabbatar da kwanaki kadan kafin a tafi Zabe aka gurfanar da Alhaji dikko inde tsohon shugaban kwastam na kasa.a gaban kotu Akan zargin. Bacewar bilyan daya a hukumar ta kwastam.
Kila wannan ya sa.dikko inde ko zaben bai halarta ba a mazabarsa ta musawa.
Dikko inde dan PDP ne .har takara akayi niyyar tsaida shi.kuma kanen sada inde yayi takaraa a PDP.a zaben da aka kammala.
Haka ma tsohon gwamnan na katsina Ibrahim shema .sau uku jami an tsaro na gayyatarsa a Abuja da Kaduna. Ana sauran kwanaki zabe.Ana sauran kwana biyu zabe.EFCC sukayi ma gidansa dirar mikiya.hatta hukumar da ar ma aikinta CCB. ba a barsu a baya ba.suka zo wajen shema suna neman ya tabbatar masu abin da ya rubuta a fom din haka yake?
Shema ya tabbatar wa da taskar labarai, wannan wa ni tattauna ta bidiyo da sukayi-( yau zamu saki bidiyon)
Hatta Dan takarar majalisar tarayyaa.a kurfi/dutsinma.Nura amadi kurfi Allah ya tsare shi.ana gobe Zabe.aka so kamashi bisa zargin wai ya boye kudin Zabe a gidanshi.
Amma a legas motar banki aka dauko hotonta ta shiga gidan Bola Tinubu.ta kai masa kudi.a ranar zabe da yan jarida sukayi masa tambaya Akan kudin .sai yace kudinsa ne…aka kawo masa sai me?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here