“SHAGO DA DAN DUNAWA” SHAHARARRUN YAN DAMBEN NAN A GUSAU A SHEKARAR 1957

0

“SHAGO DA DAN DUNAWA” SHAHARARRUN YAN DAMBEN NAN A GUSAU A SHEKARAR 1957.
Shago Da dandunawa wasu shahararrun yan dambe ne da akayi a kasar Hausa, wadanda suka sha karawa da juna har takai ga sun dauki alkawalin ba zasu kara was an dambe da juna ba.
Akwai lokachin da Dan Dunawa yaje kano suka kara da shago,yawanchin mutane suna zaton shago zaya buge dandunawa, amma sai lamari ya chanza a inda shagon ya sha wuya kamar yadda muka gani a jaridar gaskiya tafi kwabo ta shekarar 1957.
A chikin hoton za’a ga Dandunawa a hannun hagu da shago a hannun dama, da Malam Dogonyaro, watau shugaban direbobi na gusau a tsakiyar hoton,sai makidin dandunawa a hannun hagu rike da kotso.
Allah ya gafarta masu da dukkan musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here