ANYI BABBAN KAMU
‘Yan kato da garo (Civilian JTF) reshen karamar hukumar Bama jihar Borno sun kama wannan kasurgumin kwamandan Boko Haram wanda ya addabi yankin Bama mai suna Modu Hajja Bunaye Bama, kuma yana daga cikin kwamandojin Boko Haram da ake nema ruwa a jallo
A yawancin hari da ‘yan Boko Haram suke kaddamarwa a yankin Bama da Maiduguri yana daga cikin wadanda suke jagorantar harin, hatta harin da Boko Haram suka kaddamar a Jiddari Polo Maiduguri satin da ya gabata ranar da za’a gudanar da zaben shugaban Kasa yana daga cikin wadanda suka jagoranci harin
Alhamdulillah Modu Hajja Bama ya shiga hannu, karshen zalunci da ta’addancinsa yazo, kama wannan rikekken ‘dan ta’adda nasara ne daga Allah, muna jinjina ga Civilian JTF, Allah Ya kara muku taimako da nasara akan ‘yan ta’adda
Daga≠ Datti Assalafiy