Yan Ina Da Kisa Sun Kashe Mutane Biyar A Kauyen Giwa

0

AL’UMMAR garin Sabon Sara da ke gundumar Kidandan cikin karamar hukumar Giwa sun gamu da matsalar yan Ina da Kisa inda suka zo cikin Daren jiya Juma’a misalin karfe biyu saura yan mintuna suka rika yin Harbin kan Mai uwa da wabi.

Kamar yadda wakilinmu yaji ta bakin shaidan Gani da ido Mai suna Yahaya Umar ya tabbatar wa wakilinmu cewa ba tare da sani ba Sai dai kawai suka ji miyagun na harbe harbe ta ko’ina a cikin garin na Sabon Sara ga shi kuma dare ya rigaya ya yi karfe biyu saura.

Yahaya Umar ya ce sakamakon wannan kwanton Baunar da suka yi Sai da suka kashe mutane Biyar da aka yi masu jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar da ranar yau Asabar.

Sun kuma yi wa mutane Takwas rauni da Bakwai suke kwance a gadon asibitin Kauran Wali da ke cikin Birnin Zariya, yayin da daya daga cikinsu ya samu karaya a kafadarsa aka ta Fi da shi domin yi Masa dorin gargajiya bayan an kammala duba shi a asibitin.

Rahotanni dai daga garin na Sabon Sara sun tabbatar da mutuwar wata mata Mai suna Malama Fatima Ahmad da ta mutu sakamakon fargabar harbe harben karar bindigar da ta rika ji, nan take hawan jininta ya tashi ta kuma ce ga garin ku nan, ita ma an yi jana’izarta tuni.

Sai kuma wani mutum Shima da hawan jinin ya buge shi duk sakamakon fargabar da ya samu Shima yana asibitin na Kauran Wali.

Wadanda suka mutun sun hadar da Lawal, Ibrahim, Tukur da Umar da kuma Lawal da dukkan su tuni aka yi jana’izarsu baki daya.

Kamar yadda wakilinmu yaji daga bakin Yahaya Umar cewa a watannin baya ma cikin shekarar da ta gabata watannin shida zuwa Bakwai Sai da aka kawo masu hari a Gonakinsu wanda suna Gona suna aikin gyaran amfanin Gona aka farmasu nan ma an kashe mutanensu har Bakwai.

Sakataren karamar hukumar Giwa Alhaji Usman Isma’il ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce har shugaban karamar hukumar ta Giwa ya halarci jana’izar Mutanen Biyar da suka mutu sakamakon harin na Daren jiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here