DAN takarar Gwamnan Jam’iyyar APGA a Jihar Kaduna Dakta Polycarp Gankon ya bayyana wa duniya aniyarsa na marawa Dan takarar Gwamnan Kaduna karkashin PDP Honarabul Isa Muhammad Ashiru baya a zaben Gwamna Mai zuwa.
Dakta Polycarp Gankon ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da ya kira a kaduna, inda ya ce yana bayyana wa dimbin magoya bayansa da sauran jama’a cewa dukkan su a ranar zaben Gwamna Mai zuwa su tabbatar sun zabi Dan takarar Gwamna karkashin PDP domin ya dare kujerar Gwamnan Jihar kaduna.
Ya ce “Jam’iyyar Liberation Movement (ILMP) tare da Jam’iyyar APGA sun taru baki daya kuma sun yanke hukuncin marawa Jam’iyyar PDP tare da Dan takarar Gwamnati baya a zaben Gwamna Amma dai akwai yan takarar da suka tsaya takara a matakin majalisun Jiha har su Tara a kananan hukumomi daban daban don haka yayan Jam’iyyar APGA su zabe su , kuma a zaben Gwamna su jefa wa Dan takarar PDP kuri’arsu”.
Da akwai kananan hukumomi irin su Giwa,Zariya,Birnin Gwari, Chukun da kajuru tare da karamar hukumar Kaura duk akwai yan takarar APGA a matakin yan majalisar Jiha don haka a tabbatar an zabe su.
Ya kuma kara da cewa sun dauki wannan matakin ne ba wai domin wani Ko wasu sun ba su komai ba, hasalima ya tabbatar wa manema labarai cewa “Ko shi Isa Ashiru da ke takara a PDP ba su yi magana da shi ba don haka Jam’iyyun biyu sun yanke hukuncin ne domin radin kansu kuma ba su da wata manufa Sai ta ceton Jihar kaduna domin fita daga halin da ake ciki”.
“Yaku yan jarida inason kuje domin tambayar Dan takarar PDP Isa Muhammad Ashiru Kudan Ko ya san da daukar wannan mataki da na yi na mara Masa baya a zaben Gwamna”. Inji Polycarp