LABARIN MAI SOSA ZUCIYA DA SA HAWAN JINI GA YAN JAMIYYAR PDP MASU KAUNAR TA

0

LABARIN MAI SOSA ZUCIYA DA SA HAWAN JINI GA YAN JAMIYYAR PDP MASU KAUNAR TA

Labarin da na samu wanda yake yawo a baku nan Jama’ar Katsina tun Monday bayan zaben da ya gabata shine dan takarar gwamnan Katsina a karkashin tutar Jamiyyar mu ta PDP Sen. Yakubu Lado Dan Marke ya cakare kudin shi ya kama gaban shi.

Lokacin da labarin nan yazo gareni, ban yarda ba. Rashin yarda ya zo ne daga sanin da nayi na cewa shi dan takarar yana son takarar kuma yana da wani yakinin cewa shine zai lashe zaben.

Da farko lokacin da shugaban jamiyya ya ce nine Agent din Yakubu a lokacin da suka yi primary da Arc. Ahmed Aminu, nayi hira da Yakubu ya nuna mani cewar duk shiri na cin zabe ya gama shi. Har ya fada mani cewar ya ajiye zunzurutn kudi N6bn domin zaben da sauran tanade tanade.

Haka kuma Lokacin da muka hadu dashi a Portharcourt, bayan ya zama dan takara, ya fada mani cewar duk wani abu da zai yi domin ya zama gwamna ya gama yin shi kuma yana da tabbacen shi zai yi nasara. A lokacin na tuna mashi da cewar yayi ma shuwagabanin Jamiyya alkawlin N1m ko wanenen su da mota idan suka zabe shi a wajen zaben fitar da gwani Amman har lokacin bai cika ba. Ya fada mani cewa zai cika idan yaci zabe. Na ce masa distinguish idan baka ci ba fa? Sai kawai ya tashi daga inda muke zamne ya kama yin waya.

Bayan mun dawo daga zaben wanda zai yi ma jamiyya takarar shugaban kasa Allah ya ba Atiku, sai labari ya zo mana daga gidan Atiku Abubakar cewa Sen. Lado da wasu yan takara sun tafi wurin Atikun suna so a basu kudin da zasu fara yin campaign. Nayi kokarin na tuna ma Yakubu cewar idan muka yi Tsari mai kyau, N6bn ta ishe mu cin zabe ba tare da mun fita neman kudi daga wani wuri ba.

Ko da yake neman taimakon campaign ba laifi bane, Amman tunda cewar an kawo Yakubu takara ne domin ance shine ke da kudin da zai iya cin zaben shi, duk sauran yan PDP masu Basira da ilimi wadanda suka yi amfani da kudin su suka raya jamiyya basu da karfin takara bai kamata Yakubu na yawon neman abinda zai yi takara ba daga wasu.

Mu dai da muka fara bin Ladon Anyi mana hanunka Mai sanda, an ja Mana kunne, an gargade mu, an tabbatar mana abinda ya faru can baya Amman dai muka ce shi ke da kudi. Kuma shi Shema ya kawo.

An tabbatar mana Sen Lado Dan Marke ba Dan takara abin dogaro bane, don yanada record din sayarda ticket din takara ya amshe kudinsa yayi gaba muka ce munji mun gani.

Yanzun ta tabbata son zuciya da matsolan ci irin na Barr shema shi ya kawo jamiyya da mu yan jamiyya a matsayin da muke yanzun.

An fada mana shi Shema baya son kashe kudin alhihun sa ne ya sa yayi kunnen uwar shegu da shawar warin da aka bada game da wanda ya kamata yayi ma PDP takara.

Sen Lado Dan Marke bai san san darajar mutane, baya da cikkaiyar sanin mulki, baya da natsuwar da zai iya gwamna. Baya da ilimin da mutane zasu dube shi dashi su zabe shi. Bashi da sanin ya kamata, baya jin shawara, kuma ya dauki kujerar gwamna hanyar samun kudi kamar yanda aka ce ya na cewa idan yayi gwamna sai yafi Dangote kudi.

Yanzun dai ya tabbata ya cakare kudin takarar shi ya kama gaban shi.

Da farko dai Muna da tabbacin cewa campaign din Atiku ya bashi kudin yin zaben da ya gabata. Wata majiya ta tabbatar cewa a cikin kudin, am rage N600m wadda za’a yi zaben gwamna da su. Amman a bisa dukkan alamu, baza’a sa kudin a zaben ba. Wani na kusa da Yakubu ya fada mana cewa sun ce kudin sallamar su ne. Har ma anyi kaso. Shi tunda yayi hidima da kudin shi har da yin dunkuna, ya dauki N350m, mai bi mashi ya tashi da N100m babban kuwa ya dau N150m saboda hidimar da yasha.

Yanzun kuma sun dukufa neman abinda zasu samu daga gwamnati.

Wani labari mai zafi da tushe mai karfi, ya nuna Yakubu ya garzaya wajan Alh Sani Zangon Daura da Alh Sama’ila Isah Funtua su share masa fage don ya amshi kudin da ya kashe wajen kamfen dinsa idan an kafa gwamnati kuma abashi mukami kamar yanda yayi a 2011. Amman an ce sun fada mashi cewar Shugaba Buhari ba zai yarda da janye takara a kan sharadi ba. An ce sai dai idan zai janye ba tare da sharadi ba na kudi da na mulki. Masu bada labari sun ce ya nemi a hada shi da gwamna Masari domin a bashi abinda za’a bashi. Ya nuna cewa idan ya janye takara, jamiyyar APC ba sai ta kashe kudi wurin sa agent da sauran kudaden da aka saba ba. Yace ko rabin abinda za’a kashe wurin aikin zaben aka bashi shi zai janye. Wannan tunani da yayi na amsar abinda aka yi ma masu aikin zabe tanadi yana daya daga cikin rashin tausayin shi a rayuwa.

Koma me ke nan, muna jiran mu ga haduwar su da Masari ko shi zai yarda ya sallami Yakubun ko a’a. Tuni dai har ance Yakubu ya amshe duk kayen campaign da ya bada. Ya kuma SA ana sauke Posters da billbod da aka lika masu dauke da hoton shi da na Shema.

Allah ya raba jihar Katsina da jamiyyar PDP da ire iren su. An sami labari saga shafin Lawal Audi Yar’adua (Dan ade)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here