TSOHON KAKAKIN MAJALISAR KATSINA YACI KUDIN ZABE

0

TSOHON KAKAKIN MAJALISAR KATSINA YACI KUDIN ZABE.!
Daga taskar labarai
Jaridar taskar labarai ta samu tabbacin cewa rundunar yan sanda ta tsare tsohon kakakin majalisar jahar katsina. Alhaji Ali sabi u muduru.har na tsawon kwanaki biyu Akan tuhumar .karkatar da wasu kudi da aka bashi don hidimar zaben shugaban kasa da ya gabata
Bincike na taskar labarai ya tabbatar da cewa an bashi kudin Wanda yawansu ya kai miliyan biyar don gudanar da wasu ayyuka dasu a mazabarsa ta karamar hukumar mani amma ya karkatar dasu
Masu aikin sukayi aikin,amma yaki biyansu hakkinsu.Akan haka koke da korafi ya tashi.har aka kamo wani kansila Wanda kansilan ya bada Bahasin cewa dubu dari biyar Kacal aka bashi,kuma yayi bayanin abin da yayi dasu.
Daga nan yan sanda suka kamo Dan majalisar na karamar hukumar Mani.ali sabi u muduru. An tabbatarwa taska cewa da yazo bai musanta ko wahalar da shara a ba..amma ya Nemi a bashi dama ya rubuta .takardar alkawali yaje ya kawo kudin,zuwa wani lokaci
Yan sanda suka ce, Sam,ko kudi,ko su tsare shi bayan kwana uku su kaishi kotu.daga can sai gidan yari.
Da Wanda ake zargi yaga hatsarin dake gabansa.ga Zabe kuma yana takarar Dan majalisar jaha..ance sai ya jinginar da wata kaddararsa aka kawo kudin sannan ya samu yancinsa daga wajen yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here