GARURUWAN DA SUKAYI MAGANIN BARAYIN SHANU

0

GARURUWAN DA SUKAYI MAGANIN BARAYIN SHANU
Daga Taskar labarai
Wakilan taskar labarai na jahar kaduna sun kai ziyara wasu garuruwa a yankin birnin gwari ,wadanda suka hada kansu sukayi maganin barayin shanu a sashensu.
Garuruwan sune KUYELLO da LAyin dan auta
Wakilan sun gani da idanunsu yadda kusan kowa ka gani da bindigar ta gargajiya tare dashi.
A yankin rike bindiga ba laifi bane ga dan gari wanda aka sanshi.
Amma in bako ne, sai an tuhume shi
A yankunan sun tsara kansu akwai masu gadi da dare akwai masu gadin Rana akwai kuma wadanda suke bada tallafin kudi da abinci ga masu gadin.
A layin dan auta.an samu wasu makera wadanda suka kware wajen kera bindiga ta bature su sarrafa ta zuwa ta gargajiya.
Wakilan taska sunga wata irin bindiga.wadda ta gargajiya ce amma zata iya sakin harsasai goma sha hudu a lokaci daya.in an harba ta
Wakilan taska sunga wata irin bindiga da aka sarrafa wadda zata iya harba luloli ashirin zuwa talatin a harbawa daya…
A garuruwan kuyallo da layin dan auta mutanen yankin sun daskare ko a rayu ko a mutu.
Duk wani bako abin zargi ne, amma dan gari kowa na zaman cikin shiri.
Wani lokaci.hakanan mutanen garin sai su shiga dajin neman barayin na shanu
Mutanen yankin sukan sayi bindigu don ba yan sa kai.wani lokaci suyi karo karo.na sayen bindigu na zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here