KANSILAN MAZABAR KANGIWA KENAN HON USMAN YUSUF SAULAWA

0
615

DAGA RABIU SANUSI KATSINA.
An bayyana kantoman riko na karamar hukumar katsina Hon, Abu Bako Kari, a matsayin jagora nagari.
Kansila mai wakiltar mazabar Kangiwa Hon,Usman Yusuf Saulawa ne ya bayyana haka a wata ganawa da wakilin Taskar Labarai.
Saulawa yace matsayin Abu Kari na shugaba nagari ne yasa mai Girma gwamna Masari ya damka ma shi jagorancin karamar hukumar katsina, Saboda nagartar shi.
Ya kuma bada tabbacin zuwan Kari ne aka Samar ma yara gurbin karatu zuwa college of Administration da ke karamar Hukumar funtuwa akalla sunkai mutum xari da talatin 130, sannan ya dauki nauyin registration da na su da kama ma su gurin zama,bayan haka wadanda ma ba su gama sakandire ba aka maida su dan su gama tare da sa ido akan su.
Bayan haka zuwan shi ne ya tara mata kimanin dari hudu yaba su tiyar masara tiya 20-20 da naira 5000 dan su ci abinci.
Usman yakara da cewa a mazabar shi ta Kangiwa Ward, yasamar da ruwan sha agurare kamar yammawa, kofar gidan sarkin tsafta,qofar soro da gyare-gyaren borehole borehole da dai sauran wa su yankunan mazabar shi ta Kangiwa Ward.
Saulawa ya tabbbar da cewa ya bada gudunmuwa wajen gyaran wutar lantarki a yankunan shi tare da canza turakun wutar lantarki da wayar wuta a wa su sassa na Kangiwa,sannan bangaren Samar da ilimi bayan qoqarin da kantoma ya yi na mutum dari da talatin shima yasamar ma mutum sha ukku adimition zuwa college of administration a yankin shi, sai bangaren Samar da ayukan yi ga matasa yasamar ma mutum 13 casuals Wanda su ke amsar naira dubu goma goma duk wata,idan aka juya bangaren gyaran hanyar ruwa nan ma ya taka rawar ga ni inda yace ba shi yakamata yafadi ba jama’ar yankin shi ne za su iya yanke hukunci.
Daga karshe ya bayyana cewa karamar hukumar katsina da mazabar Kangiwa Ward sun shirya tsaf dan ganin sun fito kwan su da kwarkwatar su wajen marama mai girma gwamna baya kamar yadda sukayi ruwan kuri’u ga mai girma shugaban qasa Muhammadu Buhari,haka za su zubama mai girma gwamna shima ruwan kuri’a,sakamakon baida wani abokin karawa a zaben da zai gudana ranar asbar,saboda ayukan alkhairi da ya shimfida a jihar katsina ya sa ko wa ye fito to kuri’ar katsinawa ta gwamna Masari ce ba bu wanda ya cancanta sai shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here