WANE HALI DALIBAN DA SUKA CI ABINCIN A MAKURDA KE CIKI.?
Daga Taskar labarai
A jiya talata wakilan taskar labarai sun sake komawa makarantar firamare ta MAKURDA inda wasu dalibai suka ci abinci. Suka shiga wani hali.har aka kaisu asibiti,
Wakilan da suka je makarantar sun taras duk daliban sun wartsake har sun komo makaranta kwana daya da faruwar lamarin.
Taska labarai ta gano cikin yaran da aka ba abinci su fiye da dari .yara biyar ne lamarin ya shafa Wanda nan da nan da faruwar abin .aka kaisu asibitin MAKURDA, daga nan aka dauke su zuwa asibiti na Ajiwa.daga can aka maida kowane dalibi gidansu.
Jami an asibitin MAKURDA sun shaidawa taska labarai cewa, matsalar tafi kama da nasaba da yaran sunci abinci kafin su wanke hannayensu.domin bayan abubuwan azuzuwan makarantar mutane na kashi da fitsari.don haka akwai datti sosai a wajen .ana kawo abincin yaran ba ruwansu da wanke hannu kuma ba a kawo masu da cokali ba,don haka sai kawai su fara ci.
Wani jami in na asibitin yace ko lokacin da aka kawo yaran hannayensu.suka fara dubawa inda suka Ganshi kaca kaca da datti…ga kuma dankon abinci a jikinsa.
Wani jami i a asibitin ajiwa ya tabbatar wa da taska Haka cewa lamarin yafi dangantaka da Rashin wanke hannu .domin hannun yara kaca kaca.da datti kuma ga abinci sun ci da hannun mai datti.
Don haka ya roki hukumar makarantar ta tilasta kawo cokali in har za a baiwa yaran abincin.
Mun kewaya makarantar muka ga gaban makarantar fes yake.amma bayan azuzuwan yaran cike yake da dattin kashi, fitsari da sauran bola
Taskar labarai ta gano, abin na faruwa,desk ofisa,na makarantun Muhammad Abubakar MAKURDA ya isa makarantar kuma ya tsaya sai da yaga kowane dalibi an Sallame shi daga asibiti kuma an maida shi gida.
A jiyan ES na karamar hukumar Rimi, Alhaji Salisu shuaibu ibrahim ,ya je makarantar tunda safe.ya ga na da malaman makarantar. Ya kuma bi azuzuwan daliban. Ya kuma je gidansu.don ganawa da iyayensu.
Es din ya umurci masu kawo abin abincin su rika hadowa da cokulla ya kuma ce ayi wani tsarina duk dalibi sai ya wanke hannunsa kafin a bashi abincin sa.
Ya kuma sa masu gadi su sa ido akan masu zuwa suna kashi da fitsari da zubar da najasa.a bayan azuzuwa na yaran.