AN NADA FARFESA SOKEFUN A MATSAYIN MUKADASHIN MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR KARATU DAGA GIDA (NOUN)
Majalissar zartar wa ta jami’ar Karatu daga hida (Noun) ta zabi Farfesa Justus Adedeji Sokefun a matsayin sabon mukaddashin shugaban jama’ar a bangaren mulki.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabi Daraktan yada labarai na jami’ar Malam Ibrahim Sheme ya bayyana cewa Farfesa Sokefin ya samu nasara ne a zaben da majalissar zartawar ta gudanatpr a ranar 5 ga wana uku shekarar 2019 a jihar Legas in da Sokefun ya samu kuri’a 48 wanda ya sa ya samu nasara kan abokin takararsa mai kuri’a Farfesa Gbenga Ojo wanda shi kuma ya samu kuri’a 18.
Kafin zabarsa a matsayin mukadasshin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sokefun shu ne babban darakatan da ke kula da shiyyar karatu ta jami’ar da le Legas.
Ya samu digirin sa na farko a fannin shari’a a jami’ar Ife wadd yanzu ta koma Obafemi Awolowo a shekarar 1984.
Daganini sai ya tafi makarantar horas da lauyoyi a tsakanin shaekarar 1984-1985 in da ya samu lasisin zama cikakken lauya. Ya samu digiri na biyu a jami’ar Legas a shekarar 1989.
Ya fara aiki ne a matsayin mai taimakawa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria tsakanin 1985-1986
A shekarar 1987 Sokefu ya fara aiki a jami’ar jihar Ogun (Jami’ar Olabisi Onabanjo) har zuwa shekarar 2007.
Daga cuikin nasarorin da ya samu a fannin aiki sun hada da zama mai ba ministan shari’a shawara na musamman saga shekarar 1993-1994 a lokacin ya na da kuruciyarsa sosai.
Bayan kammala wannan aikin Sokefun ya zama mukadasshin tsangayar shari’a a jami’ar jihar Ogun daga 1994 zuwa 1997. Daga nan kuma ya zama shugaban sashen Shari’a na jami’ar daga shekarar 1997 zuwa 2000.
Daga nan kuma sai ya zama shugaban tsangayar shari’a ta jami’ar jihar Ogun daga 1997 zuwa 2007.
Ya fara aiki a Jami’ar Karatu daga Gida (Noun) a matsayin Farfesa a shekarar 2007.
Ya zama shugaban tsangayar shari’a a jami’ar Karatu daga gida daga 2007 zuwa 2010. An kara zabar shi a matsayin shugaban tsangayar ta shari’a daga shakarar 2013 zuwa 2016. Sokefun ya bayar da muhummiyar gudumuwa wajen cigaban jami’ar Karatu daga gida a fagage mabanbanta.
Haka kuma ya bayar da gudumuwa wajen cigaban kasar nan a wurare da dama da suka hada da; mamba a kwamitin kare hakkin dan Adam a ma’aikatar shari’a ta kasa daga 1993-1994 da mamba a kwamitin kare hakkin dan Adam a jami’ar Olabis Onabanjo da ke Ogum daga 1999 zuwa yau.
Sokefun ya zama Farfesa a Jami’ar Karatu daga Gida (Noun) a 2007.
Haka kuma shehin malami ne dake ziyartar jami’o’i da dama domin bayar da darasi,wadanda suka hada da Jami’ar Gambiya 2009-2012 shugban masu diba jarabawa na waje a jami’ar Kasa ta Rawanda daga 2009-2014 Dangaladiman Farfesa a jami’ar kasa da kasa ta Wisconsin da ke kasar Ghana. Daga 2013 zuwa yau da kuma jami’ar Crescent da ke Abekuta daga 2011 zuwa Yau.
Haka kuma mai diba jarabawa ne na waje a Cibiyar Fetur da dokokin iskan gas da ke jami’ar Ibadan daga 2013 zuwa yau.
Sekefun memba ne a fitattun kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan wadanda suka hada da Kungiyar Lauyoyi ta kasa da kungiyar lauyoyin kasa da kasa reshen Najeriya. Da sauransu.
Ya rubuta litattafai da makalu da dama a mujallu da jaridun kasar nan.
Farfesa Sokefun yana da aure da da ‘ya’ya da jikoki.
Sa hannu
Ibrahim Shema
Daraktan yada labarai
Jami’ar Karatu daga gida (NOUN)