KURFI DA DUTSIN-MA: DAN MAJALISAR TARAYYA MAI BARCI?

0
518

KURFI DA DUTSIN-MA: DAN MAJALISAR TARAYYA MAI BARCI?

Daga Taskar labarai

Daga cikin ayyukan da jaridar Taskar labarai tayi a ranar zabe, shi ne zuwa rumfunan zabe, ganawa da manyan yan takara, da kuma manyan ‘yan siyasa don su fadi ra’ayinsu, akan ya suka ga zaben.

Bayan rahotanni na rubutu Taskar labarai har bidiyo tayi na rahoton musamman akan zaben, wanda kuma yayi yawo sosai a yanar gizo.

A ranar zaben shugaban kasa, wakilan mu, sun yi magana da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa, Hadiza Bala Usman. Da mutane irinsu Dakta Kabir Matazu ciyaman na UBEC Abuja, da Bala Abu Musawa da Attahiru Bala Usman da tsohon gwamnan Katsina Ibrahim Shema da da sauransu.

A ranar munje Dutsinma. Inda muka so ganawa da Dan majalisar da ke takara a lokacin ta kujerar Kurfi da Dutsinma (Yayi nasara)

Muka je, har gidansa aka ce mana tun da ya jefa kuri’arsa ya dawo ya kwanta kuma yace kar a kuskura a tayar da shi sai lokacin tashinsa, karfe shidda na yamma kamar yadda ya saba.

A ranar zaben gwamna na 9/3/2019 wakilan sun sake fita inda suka gana da Alh Dikko Radda DG Smedan da Ibrahim Shema tsohon gwamnan jihar Katsina da Alhaji Umar Tata da Alhaji Kabir Barkiya zababben sanata da Hon Danlami Kurfi da mataimakin gwamnan Katsina Arc Mannir Yakubu da sauransu.

A ranar ma mun sake komawa gidan zababben dan majalisar tarayyar Kurfi da Dutsinma aka sake shaida mana cewa, ya kwanta bayan da dawo daga jefa kuri’arsa amma in har muna son ganinsa mu dawo bayan biyar na yamma lokacin ya tashi, ya sauko daga kan bene.

Mun buga wayarsa muka ji ana amfani da ita muka ce lallai ba barci yake ba, sai wani dan bangar siyasa da ya san gidan yace ga shawara ya nuna wata tagar bene da irin gilas din nan ina ganinka baka ganina yace daga can yakan lekowa yaga masu son ganinshi in yana son ganinsu ya fadawa masu gadi, in kuma bai so, yayi likimo don haka ku zauna mintuna kadan in kaga ba a bude kofar nan ba yi ta kanka.

Mun jira shiru muka tafi an tabbatar yana gidan yana rumtsawa don lokacin barcinsa ne, kuma ba mai iya tada shi yana a sama inda ba mai isa wajen sai ya safko.

Armaya’u dan kasuwa ne da yake samun nasara a kasuwancinsa saboda jajircewa da tsare gaskiya da Amana da kuma an shaide shi mutumin kirki ne da taimakon wadanda sukayi nasarar fada masa matsalarsu.

Amma rayuwar siyasa ba tasa bace, bincike na Taska ya gano takarar ma tilasta masa aka yi ba domin yana so ba.
Mutum ne, Wanda harkarsa kawai ta dame shi ba ruwansa da hidimar kowa, wannan ya sa masa mutunci a Dutsinma da wadanda suka san shi.

Wadanda suka jawo shi siyasa yana da kyau su fara masa darasi na rayuwar dan siyasa da kuma rayuwar wanda aka ba mukamin siyasa da wanda yake zababbe a siyasa.

Su zaunar da shi su fara biya masa a allo yana karantawa da harda kuma kar ya wanke sai ya nakalce shi.

Ya yi maza ya iya wannan kafin ya tafi majalisa inda karatun zai karu zai hada harda na iya zaman majalisar don wakiltar wadanda suka turoshi.

Wadannan bitar karatusuna da muhimmaci, don sauke nauyin da ya dauka sannan ya kare mutumcinsa da ya gina.
In kuma ba haka ba, za a bata uku daya bata gyaru ba…..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here