DARUSSAN SIYASA DAGA ZABUKAN KANO

0

DARUSSAN SIYASA DAGA ZABUKAN KANO.

Daga shafin Bello Muhammad Sharada.


Jiya bayan isha’i hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kano ta bada sanarwar zata sake bada damar zabe a wasu gurare. Sai an sake zaben sannan za a gano wanda ya samu cikakkiyar nasara a kan kujerar gwamna.

Ba nufi na bane na fadi dalilin da jam’iyyar A ko B ta samu nasara ko matsala ko kuma hujjojin faduwa ko dacewar Mallam Wane ko Alhaji Wane.
Wannan zai zo nan gaba da yardar Allah bayan an kammala duk zaben, an fadi ainihin wanda Allah ya baiwa.

Na tsinto mana wasu darussa ne a fagen siyasa da zabukan da aka yi suke koya mana. A wajen fitar da wanan tsokacin ina la’akari da abubuwan da suka faru a zabukan shekarun 2003 da 2007 da 2011dana 2015.

Zamu iya daukar darasi goma sha biyu daga wadannan zabukan.

NA DAYA: Halin dan takara da dabi’unsa da salon tafiyar da mulkinsa shi ne awon farko da masu zabe a Kano suke yi. A shekarar 2003 da shi suka yi amfani wajen sauke Kwankwaso, a 2007 haka suka yi wajen maimaicin Shekarau, a 2011 shi ne dalilin dawowar Kwankwaso, tasirinsa ne ya shafi Ganduje a 2019. Duk girman ayyukan gine-gine da raya kasa da mai gwamnati zai yi kuma yake son tazarce ba zai hana shi faduwa ba.

NA BIYU: Mutanen Kano a wajen zabe gida biyu suke rabuwa. Ba sa yin jam’iyya ta uku, har ta kama mulki, amma suna zaben jam’iyyu barkatai. A 2003 Dan Hasan ya ja kuri’u a PSP, Ibrahim Little ya ja a PRP. A 2007 AC ta ja kuri’u masu yawa, a 2011 CPC da ACN sun yi tasiri, a 2019 PRP ta ja kuri’a. Zaka iya shiga wata jam’iyya amma amma ba za a baka kuri’ar cin zabe ba komai tsari da manufarka da irin salon da ka yi amfani da shi a kamfen. Jam’iyya ta uku, gaskiyar magana ta ‘yan fancale ce.

NA UKU: Komai karfin gwamnatinka, zaka iya faduwa zabe a Kano, kudi ba sa yin tasiri, haka tsiya-tsiya. Da mulki da kudi ba sa hana Kanawa zaben ‘yancinsu. Kwankwaso ya samu mulki a karo na farko a shekarar 1999 ba shi da kudi da mulki, Shekarau ya samu mulki a shekarar 2003 ba kudi ba mulki, Abba K Yusuf a zagayen farko ya samu nasara ba kudi ba mulki a 2019. Da Kwankwaso da Shekarau duk sun fadi zabe suna da dukiya da mulki a hannunsu.

NA HUDU: Jajirtacce kuma mai tsari in ya shiga jam’iyya ta daya ko ta biyu a Kano yana samun dacewa. Jajircewar Kwankwaso ce ta bashi damar dawowa a 2011, ita ta baiwa Abba Gida Gida nasarar 2019. Haka kuma fadi tashin Shekarau da jajircewar ayarin ‘yan tafiyarsa ita ta jawo nasararsa a 2003.

NA BIYAR: Mutanen kwaryar birnin Kano tun shekarar 2003 ba sa zaben mai gwamnati. Sun yi haka a 2007 da 2011 da 2015 da 2019. Su kuma mutanen karkarar Kano a wajen zabe suna bin tsarin wanda yake kan mulki. Wannan zaben har take aka rika yi masa, ‘yan birni suna bugawa da ‘yan kauye.

NA SHIDA: Kananan hukumomi takwas da Dala da Nassarawa da Kano Municipal da Fagge da Gwale da Ungoggo da Tarauni da Kumbotso na tsakiyar birnin Kano sune suke yanke wanda ke cin gwamna a Kano. In ka fadi a cikinsu ka fadi zabe, in ka yi nasara a cikinsu ka ci zabe. Zabe biyar da aka yi haka ce take faruwa.

NA BAKWAI: Manyan ‘yan siyasa da suka yi shuhura a wajen zabe ba su cika tasiri ba a zaben da ba sune da kansu suka tsaya ba. Misali a zabukan duk da Kwankwaso ya tsaya da kansa ko Shekarau da kansa duk suna nasara. Amma suna faduwa in sun ce a bi wani. Hakan tana faruwa a kan irinsu Mustapha Bakwana da Aminu Dabo da Hafizu Abubakar da Bala Gwagwarwa da Dan Zago da Abdullahi Abbas da Salihu Takai da Mas’udu Doguwa da Abdullahi Rogo da sauransu da yawa.

NA TAKWAS: Manyan kasa da suka shafi kasuwa wato attajirai da ‘yan boko da sarakai da malamai da tsaffin masu damara da ma’aikata ba ruwansu da jama’a na kasa a cikin sabgar zabe a lungu da mahaifarsu. Su kowa ne ne ya yi nasara nasu ne, zasu je da bukatunsu. Basu cika damuwa da duk wanda za a zaba ba komai muninsa ko kyawunsa. Suna gefe, sun barku ku ci kanku.’Elites’ nake nufi.

NA TARA: Masu zabe a Kano suna hukunta dan takara ne da fassarar da aka ba shi ko aka kalle shi da ita. Misali an fassara Kwankwanso da dan duniya jajirtacce, shi kuma Shekarau mai saukin kai, amma dan ci da addini, shi kuma Ganduje mai likimo dan rashawa. Da an yi maka tambari kuma rediyo da soshiyal midiya ta dauka, aka rera waka ko aka hau mumbarin aka shaide ka, shike nan magana ta kare.

NA GOMA: A lokacin da aka zo yin zabe a Kano wanda ya fi girman matsala da ta fito fili shi ne yafi shan wahala, koda kuwa ya tara mutane. Ganduje shi ya fi kowa shan wahala a ‘yan takarar gwamnan Kano tun 1999. Shi ne wanda matsalarsa ta fi bayyana karara kuma abokan hamayyarsa suka rika amfani da ita sosai.

NA SHA DAYA: Wanda yake cin zabe a Kano shi ne wanda ya fi tattaro kan jama’a mabanbanta zuwa bangarensa. Wato a Turance mai ‘Consensus Building’ zaben Kano abubuwa ne da yawa suke bada nasararsa.

NA KARSHE: Kano tana iya daukar kowane irin mutum kuma tana iya jefar da shi a kowane lokaci. Ba ta da gwani na dindindin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here